Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi

Rundunar 'Yan sandan Jihar Niger ta ce ta kama wani Sani Garba mai shekaru 32 a kan yi wa wata dattijuwa mai shekara 60 fyade.

A cewar jaridar Punch, Garba da rundunar 'yan sandan ta yi holensa a ranar Juma'a ya ce yadda mazaunin gyatumai ke motsi ne ke jan hankalinsa da tayar masa da sha'awa.

Wanda ake zargin ya kuma ce yana jin dadin lalata da mata masu shekaru da yawa a unguwarsu saboda ba shi da kudin neman budurwa kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Na fi jin dadin yi wa dattawan mata fyade - Wanda ake zargi

Na fi jin dadin yi wa dattawan mata fyade - Wanda ake zargi. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: An ƙwace kujerar ɗan majalisar APC an bawa PDP

Ya kara da cewa ya yi wa fiye mata masu shekaru da yawa fiye da uku fyade a unguwarsu, ya ce ya yi nadamar aikata abinda ya kira “shirme”.

"Tunda ba ni da kudin rike budurwa. Na gwammace in rika lalata da tsofafin mata a unguwar mu kuma ina jin dadin hakan.

"Wasu lokuta na kan tambayi kai na me yasa na ke aikata wannan shirmen?’Na yi takaicin tsintar kaina a wannan halin," in ji shi.

Wasiu Abiodun,Kakakin rundunar, ya ce jami'an hukumar na 'B' Division ne suka kama wanda ake zargin a Suleja da ke jihar.

Abiodun ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

An ce wanda ake zargin ya yi kuste gidan wata mata mai yawan shekaru a ranar 18 ga watan Yuli misalin karfe 4:30 na yamma kuma ya yi mata fyade.

Hakan na zuwa ne bayan yawaitan fyade da ake samu a sassan Najeriya daban daban.

A wani rahoton, kunji wasu 'yan bindiga sun sace dan sanda mai mukamin sufeta, matan wasu fitaccen mafarauci da wasu mutane biyu a garin Koma da ke jihar Adamawa kamar yadda The Nation ta ruwaito.

'Yan bindigan sun sace mutane shidan ne daga gidajensu da tsakar dare a garin na Koma da ke karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa maharan a safiyar ranar Alhamis sun kashe mutum daya da ake tunanin ya zame barazana gare su.

Rahotanni sun ce yan bindigan masu yawa sun shiga garin na Koma sannan suka fara bi gidajen wadanda suke son sacewa daya bayan daya suna daukan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel