Mata sun yi zanga - zanga tsirara a Kaduna

Mata sun yi zanga - zanga tsirara a Kaduna

Damuwa a kan yadda 'yan bindiga ke cigaba da kashe musu maza, matan kudancin jihar Kaduna sun gudanar da zanga - zanga tsirara domin nuna rashin jin dadinsu a kan lamarin.

Daga cikin matan akwai wadanda suka sanya bakaken tufafi. Dukkan masu zanga-zangar sun rankaya zuwa fadar Sarkin Atyap, Atak Njei, da ke karamar hukumar Zangon Kataf.

A cewar matan da ke zanga-zangar, cigaba da kashe - kashe a garuruwansu ya rabasu da mazajensu na aure, iyaye, 'yan uwa, da 'ya'ya, tare da mayar da mafi yawansu zawarawa.

Kazalika, sun bayyana takaicinsu a kan yadda 'yan bindiga suna kwace iko da gonakinsu, yanzu kowa tsoron zuwa gona ya ke yi saboda fargabar 'yan bindiga.

Fusatattun matan da ke zanga-zangar sun yi birgima a kasa tsirara yayin da suke kira a kan a dauki mataki tare da yi musu adalci a kan kisan gillar da ake yi wa jama'arsu.

Masu zanga-zangar sun ce suna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, gwamnati, hukumomin tsaro da kungiyoyin kasashen duniya da su kawo musu agaji tare da kubutar dasu daga mugwayen 'yan bindiga da suka hanasu zama lafiya.

Mata sun yi zanga - zanga tsirara a Kaduna

Mata masu zanga-zanga
Source: Twitter

"Muna kira ga gwamnati da ta taimakemu mu samu damar komawa gonakinmu domin noma ne hanyar samun kudin shigar jama'armu, sannan mafi muhimmanci; a kawo karshen kashe-kashe," a cewarsu.

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa cewa a kalla mutane 19 rahotanni suka bayyana cewa sun rasa ransu sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai kauyen Kukum Daji a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an kai harin ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: Yadda rundunar soji ta kama manyan 'yan bindiga 9 a Katsina da Sokoto

Kazalika, jaridar ta bayyana cewa wasu mutane 30 sun tsallake rijiya da baya bayan sun tsira da munanan raunuka.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun dira kauyen tare da yi wa mutane kisan gilla.

Mista Yashen Titus, shugaban kungiyar cigaban kauyen Kukun Daji, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa 'yan bindigar sun bude wuta a wurin wani taron biki da ake yi a wani gida a kauyen.

Ya kara da cewa 'yan bindiga sun dira kauyen da misalin karfe 10:35 na dare tare da fara yin harbin 'kan mai uwa da wabi'.

"Suna dauke da muggan makamai, mutane 17 daga cikin mutanen suka kashe sun mutu nan take a wurin da suka harbesu.

"An garzaya da mutane 32 zuwa asibiti domin ceton rayuwarsu, amma, abin takaici, biyu daga cikinsu sun mutu a asibiti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel