Yanzu-yanzu: Gwamna Fayemi ya kamu da cutar korona
1 - tsawon mintuna
Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya kamu da cutar korona bayan da ya yi gwajin cutar a karo na uku. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.
Kamar yadda ya wallafa, "Na yi gwajin cutar korona a karo na uku a jiya kuma ya bayyana ina dauke da cutar.
"A halin yanzu bana jin wata alamar cutar kuma tuni na killace kaina a gida. Ina samun kulawar likitoci a halin yanzu.
"Na nada mataimakina da ya ci gaba da tafiyar da al'amuran mulki amma zan ci gaba da wasu aiiyukan daga gida."
Asali: Legit.ng