Hadimin Gwamnan Ayade da ake zargi da laifin fyade ya fadi ya mutu

Hadimin Gwamnan Ayade da ake zargi da laifin fyade ya fadi ya mutu

- Edet Okon Asim, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Cross River kuma mai bada shawara na musamman ga Gwamna Ben Ayade, ya yanke jiki ya mutu

- Asim dai na fuskantar tuhuma a kotu inda ake zarginsa da yi wa mai aikinsa fyade

- Hadimin gwamnan ya mutu ne a jiya Talata, 21 ga watan Yuli

Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Cross River, wanda aka nada a matsayin mai bada shawara na musamman ga Gwamna Ben Ayade, Edet Okon Asim, ya fadi ya mutu a cikin motarsa.

A shekarar da ta gabata, an zargesa da yi wa mai aikinsa fyade. Har a halin yanzu ana sauraron karar a kotu.

Daga majiya mai karfi ta cikin iyalansa da abokan aikinsa sun ce, Asim ya rasu a cikin motarsa a Eta Agbo da ke Calabar a daren ranar Talata, 21 ga watan Yuli.

Hadimin Gwamnan Ayade da ake zargi da laifin fyade ya fadi ya mutu

Hadimin Gwamnan Ayade da ake zargi da laifin fyade ya fadi ya mutu
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa, an mika gawar Asim zuwa ma'adanar gawawwaki.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun damke magidancin da yayi wa diyar matarsa fyade

Idan za ku tuna, a shekarar bara ne Asim, ya shiga hannun hukumar yan sandan jihar bisa ga laifin yiwa yar karamar yarinya fyade a garin Calabar.

Jaridar Vanguard rahoto cewa tsawon shekara uku kwamishanan ya kwashe yana lalata da yarinyar.

Ya fara kwanciya da ita tun tana shekaru 12 da sanin mahaifiyarta. Ta zubar da ciki sau biyu kuma ta samu rauni a farjinta yayinda ake zubar da cikin a karo na uku.

Bincike da aka gudanar ya nuna cewa mahaifiyar yarinyar, Misis Stella ta kasance karuwar kwamishanan kuma ita ce ta bashi daman kwanciya da yar karamar yarinyarta.

Wani majiya da aka sakaye sunansa ya bayyana cewa Misis Stella ta kasance tana auren wani shahrarren fasto a Calabar wanda ya kasance abokin kwamishanan amma ya mutu. Ta haifa masa yara biyu.

Yace: "Tun bayan mutuwan faston, Mista Asim ya kasance yana taimakon iyalinsa kuma ya dade yana hakan. Fara girman yarinyar ke da wuya, sai ya fara sonta kuma yana kwanciya da dukkansu biyu (ita da mahaifiyarta)."

Jaridar Vanguard ta samu labarin cewa yarinyar yar makarantar sakandaren gwamnati dake Calabar.

Mahaifiyar ta gargadeta kada ta sake ta fadawa kowa abinda ke faruwa tsakaninta da kwamishanan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel