'Yan sanda sun damke magidancin da yayi wa diyar matarsa fyade

'Yan sanda sun damke magidancin da yayi wa diyar matarsa fyade

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta damke wani mutum mai shekaru 39 mai suna Obiora Patrick sakamakon zarginsa da ake da lalata diyar matarsa.

A takardar da ta fita daga hannun kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da yarinyar ke asibiti.

DSP Nguroje ya yi kira ga jama'a da su bada goyon baya wurin yaki da cin zarafin da sauran laifuka masu alaka ga hakan.

Ya yi kira ga iyaye da su dinga bada kulawa ga 'ya'yansu.

'Yan sanda sun damke magidancin da yayi wa diyar matarsa fyade

'Yan sanda sun damke magidancin da yayi wa diyar matarsa fyade Hoto: Daily Trust
Source: Depositphotos

Ya ce, "Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa tana sanar da jama'ar cewa za ta tsananta bada kariya ga mata da kananan yara.

"A ranar 20 ga watan Yulin 2020, ta damke wani mutum mai suna Obora Patrick mai shekaru 39 a Jimeta da ke karamar hukumar Yola ta arewa a kan lalata da diyar matarsa."

A wani ci gaba makamancin hakan, wani mutum mai shekaru 46 ya shiga hannun 'yan sanda sakamakon fyade da yayi wa yarinya mai shekaru 13.

Wata kotun majistare da ke Makurdi ta bukaci a adana shi a gidan yari.

Wanda ake zargin mai zama a lamba 54 titin Bauchi da ke yankin Wadata da ke Makurdi, ana zargin ya aikata laifin ne yayin da aka tura yarinyar tallan gyada.

Dan sanda mai gabatar da karar ya sanar da cewa, wani Abdulrazak Unuru da ke lamba 7 a titin Ejule a Wurukum da ke Makurdi ya kai wa 'yan sandan korafi a ranar 7 ga watan Yulin 2020 wurin karfe 9 na safe.

Ya ce ya tura diyarsa mai shekaru 13 tallan gyada amma a kan hanyarta ta zuwa mutumin ya ja ta da karfi zuwa cikin dakinsa inda yayi lalata da ita.

Bayanan sirri sun tabbatar da cewa an kama Alhaji Sani Hashimu a kan laifin wanda ya ci karo da sashi na 284 na Penal Code.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Mutum 8 sun rasa rayukansu a sabon rikicin Zangon Kataf

Amma kuma wanda ake zargin ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.

A lokacin da aka kira shari'ar, Alkalin ya ki karbar duk wani roko.

Ya bukaci a ci gaba da bincike sannan a adana wanda ake zargin a gidan gyaran hali zuwa ranar 9 ga watan Oktoba 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel