Yadda masu fyade suka kashe wata matashiya a jihar Neja

Yadda masu fyade suka kashe wata matashiya a jihar Neja

- Hukumar yan sandan jihar Neja ta kama wasu matasa biyu da suka yi wa matashiya fyade tare da halaka ta

- An ambaci matasan a matsayin Abdulkadir Ibrahim, mai shekaru 25 da Abubakar Idris, mai shekaru 29

- A cewarsu sun dade suna neman wanda za su yi asiri dashi don haka da matashiyar ta nemi taimako a wajensu sai suka yi amfani da damar

Rundunar yan sanda a jihar Neja sun damke wasu matasa biyu da ake zargi da hannu a aikata fyade da kisan wata matashiya ‘yar shekara 18, Hauwa Saidu.

An tattaro cewa matasan biyu masu suna Abdulkadir Ibrahim, mai shekaru 25 da Abubakar Idris, mai shekaru 29, sun fallasa cewar sun yaudari matashiyar zuwa inda suka yi mata fyade da kuma kashe ta.

‘Yan sanda sun ce wadanda ake zargin sun rage wa matashiyar hanya a kan babur dinsu amma maimakon su ajiye ta a wajen zuwanta.

Sai suka karkatar da ita zuwa wajen da suka aikata laifin inda suka kashe ta sannan suka sassare jikinta.

Yadda masu fyade suka kashe wata matashiya a jihar Neja

Yadda masu fyade suka kashe wata matashiya a jihar Neja Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Ibrahim ya ce: “Bamu san za a kama mu ba. Mun dade muna neman wanda za mu yi asiri dashi don haka da ta tunkaremu domin rage mata hanya kan babur dinmu, sai muka ga hakan a matsayin wata dama da ba za mu bari ya kubce mana ba.”

KU KARANTA KUMA: Harkallar NDDC: Tsaro ya tsananta a majalisar tarayya kafin isowar Akpabio

Kakakin ‘yan sanda, ASP Wasiu Abiodun ya ce wadanda ake zargin ne suka yi masu jagora zuwa wajen da suka aikata ta’asar, ya kuma kara da cewa ana kan bincike a yanzu.

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa tsoho dan shekara 60 mai suna, Mista Okafor Ndubuisi, ya shiga hannun ‘yan sanda kan zargin lalata ‘yar shekara 9.

Lamarin ya afku ne a karamar hukumar Oyi da ke jihar Anambra.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar wanda ake zargin ya sha lalata da yarinyar sau da dama a dakinsa.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Mohammed, ya ce yan sandan da ke aiki a sashin 3-3, Nkwelle Ezunaka a karamar hukumar Oyi, sun kama Okafor Ndubuisi kan zargin lalata yarinya yar shekara 9.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel