Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a jihar Katsina

Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a jihar Katsina

Wani abin fashewa da ake zargin Bam ne ya tashi a kauyen Yammama, a karamar hukumar Malumfashi ya jihar Katsina kuma mutane da dama sun rasa rayukansu.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne da safiya Asabar a gonar wani mutum mai suna Alhaji Hussaini Mai Kwai.

Har yanzu ba'a san ainihin adadin wadanda suka rasa rayukansu amma masu idanuwan shaida sun bayyana cewa akalla mutane shida sun mutu.

Wani mai idon shiada yace wadanda suka mutu leburori ne dake cire ciyayi a gonar.

"Na kirga gawawwaki 6 kuma an garzaya da wasu 5 asibiti. Jami'an tsaro sun killace wajen yanzu." Majiyar ta ce.

Saurari karin bayani....

Asali: Legit.ng

Online view pixel