Dalilin da yasa aka tsare Magu na tsawon kwanaki 10 - Fadar shugaban kasa

Dalilin da yasa aka tsare Magu na tsawon kwanaki 10 - Fadar shugaban kasa

Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya ce kwamitin bincike na fadar shugaban kasar ya tsare dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ne don tabbatar da cewa ba a taba takardu masu muhimmanci ba.

Adesina ya sanar da hakan ne a wani shirin gidan talabijin na Channels mai suna "siyasarmu a yau".

Hakazalika, lauyan Magu, Rosin Ojaomo, ya ce idan mai shari'a Salami ya gano cewa Magu bai aikata ko daya daga cikin zargin da ake ba, toh shugaban kasa ya mayar da shi kujerarsa.

Sai dai, Adesina ya ce shi ba lauya bane balle ya san ko daidai bane abinda kwamitin yayi na tsare Magu har tsawon kwanaki 10.

Dalilin da yasa aka tsare Magu na tsawon kwanaki 10 - Fadar shugaban kasa
Dalilin da yasa aka tsare Magu na tsawon kwanaki 10 - Fadar shugaban kasa Hoto: The Cable
Asali: UGC

Amma ya ce akwai yuwuwar wasu takardu masu alaka da binciken ne basu so a taba yayin da suke aikinsu.

Ya ce kafin a gayyaci Magu, kwamitin ya yi zama na makonni masu tarin yawa don tattaunawa a kan zargin rashawar tare da duba ko akwai bukatar ganin shi.

Ya kara da cewa "a saboda haka ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa kwamitin binciken damar gayyatar Magu don amsa tambayoyi a kan zargin da ake masa."

An damke Magu a ranar Litinin ta makon da ya gabata kuma 'yan sanda sun ci gaba da tsareshi har zuwa ranar Laraban makon nan da aka sakesa.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 4 masu muhimmanci da Magu ya fadi bayan sakinsa

Yana ta bayyana a gaban kwamitin bincike na fadar shugaban kasa a kan zargin da ake masa na rashawa da rashin biyayya ga ministan shari'a kuma Antoni janar na tarayya.

A ranar Laraba, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya sanar da Magu ta hannun lauyansa cewa ba shi ke tsare da shi ba.

Kwamitin bincike na fadar shugaban kasa ne ke tsare da shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu, ya yi magana a kan radadin da ya ji yayinda aka tsare shi.

Magu ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yanke kauna da yaki da rashawa.

Ya ce dukkanin zarge-zargen da ke yawo duk don a bata sunansa da na EFCC ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel