Ya kamata a fara dandake masu fyade - Kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila

Ya kamata a fara dandake masu fyade - Kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bada shawaran tsananta ukuba kan masu fyade sakamakon yadda kararrakin fyade ya yawaita kwanakin nan a fadin tarayya.

Gbajabiamila ya ce matsanancin hukuncin ka iya hadawa da yanke al'auran duk wanda aka kama da laifin fyade.

Premium Times ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin kungiyar yaki da fyade (MARS-V) a ofishinsa dake majalisar dokokin tarayya Abuja.

Kakakin ya ce lallai lamarin fyade ya zama annoba a kasar nan kuma kafofin yada labarai na da rawan takawa wajen yaki da annobar.

Yace: "Adadin rahotannin fyade yanzu na da ban tsoro. Mara tunani ne kawai zai yi fyade. Ni a fahimta na fyade ta zama annoba."

"Ya kamata a mayar da hankali kan lamarin fyade kaman yadda aka mayar kan Coronavirus."

"Babu wani mutum mai hankali da zai yi jima'i da yar watanni uku."

Ya kamata a fara dandake masu fyade - Kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila

Femi Gbajabiamila
Source: UGC

A wani labarin mai alaka, Yan majalisar dokokin jihar Kano sun kaddamar da shirye-shiryen sauya dokar jihar ta Penal Code (No.12), domin tabbatar da an fidiye duk wanda aka kama da laifin fyade a jihar.

Yan majalisar sun tattauna kan hakan ne sakamakon kudirin da mamba Nurudeen Alhassan mai wakiltan mazabar Rano ya shigar na bukatar sauya dokar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Kakakin majalisar, AbdulAzeez Gafasa, da sauran yan majalisan sun yi ittifaki kan lallai mai fyade ya cancanci dandaka.

KU KARANTA: Muna kan bakanmu, ba za a yi jarabawar WAEC bana ba - Gwamnatin tarayya

A ranar Talata LegitHausa ta kawo muku rahoton cewa Wata kotun Majistare dake zanne a jihar Kano ranar Talata ta yankewa wani matashi dan shekara 30, Umar AbdulRahman , hukuncin daurin watanni 24 a gidan gyara hali kan laifin lalata kananan yara maza uku.

Kotun ta kama AbdulRahman, wanda mazaunin Layin Yankifi Maidile Quarters ne a Kano, da laifin aikata ba daidai ba.

Alkalin kotun Majistaren, Muhammad Idris, ya yanke mai hukuncin daurin shekaru biyu kuma babu damar beli.

Masu sharhi sun bayyana rashin amincewarsu da wannan hukunci inda suka ce ya yi sauki da yawa kuma hakan bai zai zama izina ga masu fyade ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel