Yan majalisar jihar Kano sun yi ittifakin dandake duk wanda aka kama da laifin fyade

Yan majalisar jihar Kano sun yi ittifakin dandake duk wanda aka kama da laifin fyade

Yan majalisar dokokin jihar Kano sun kaddamar da shirye-shiryen sauya dokar jihar ta Penal Code (No.12), domin tabbatar da an fidiye duk wanda aka kama da laifin fyade a jihar.

Yan majalisar sun tattauna kan hakan ne sakamakon kudirin da mamba Nurudeen Alhassan mai wakiltan mazabar Rano ya shigar na bukatar sauya dokar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Kakakin majalisar, AbdulAzeez Gafasa, da sauran yan majalisan sun yi ittifaki kan lallai mai fyade ya cancanci dandaka.

Alhassan Yace: “Ina kira ga majalisa ta sake duba wannan domar a sauya ta, domin samar da ukubar dandaka kan masu fyade.”

”Na yi imanin cewa wannan kadai shine matakin da za a iya dauka domin kawo karshen fyade cikin al’umma saboda ya zama ruwan dare.”

Ya kara da cewa idan iyaye za su iya daina daurawa yaransu talla, da hakan zai taimaka matuka wajen kawo karshen annobar.

Ya ce yawancin masu aikata laifin na amfani da yan talla musamman a wuraren da ake aikin gine-gine.

Yan majalisar jihar Kano sun yi ittifakin dandake duk wanda aka kama da laifin fyade

Yan majalisar jihar Kano sun yi ittifakin dandake duk wanda aka kama da laifin fyade
Source: UGC

A jiya LegitHausa ta kawo muku rahoton cewa Wata kotun Majistare dake zanne a jihar Kano ranar Talata ta yankewa wani matashi dan shekara 30, Umar AbdulRahman , hukuncin daurin watanni 24 a gidan gyara hali kan laifin lalata kananan yara maza uku.

Kotun ta kama AbdulRahman, wanda mazaunin Layin Yankifi Maidile Quarters ne a Kano, da laifin aikata ba daidai ba.

Alkalin kotun Majistaren, Muhammad Idris, ya yanke mai hukuncin daurin shekaru biyu kuma babu damar beli.

Lauyan gwamnati, Badamasi Gawuna, ya bayyanawa kotu cewa iyayen Umar Tanko da Ahmad Bello, dukkansu mazauna Mundadu Quarters sun shigar da kara ofishin yan sandan Kumbotso ranar 23 ga Afrilu.

Ya ce Umaru AbdulRahman ya yi lalata da kananan yaran uku, sannan ya baiwa kowanne cikinsu N50.

Ya ce hakan ya sabawa sashe 284 na dokar Penal Code.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel