Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatad da manyan Diraktoci 12 a hukumar EFCC

Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatad da manyan Diraktoci 12 a hukumar EFCC

Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da manyan Jami’an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, yayinda bincike ke cigaba da gudana kan Ibrahim Magu.

Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana wa PM News a daren Talata cewa babban sakataren hukumar, Olanipekun Olukoyede , na cikin wadanda aka dakatar.

A cewar majiyar, an dakatad da su ne bisa laifuka daban-daban na almundahana da rashawa.

An dakatad da su ne domin bada damar gudanar da bincike ba tare da wani cikas ba.

Majiyar tace: “An dakatad da dukkan jami’an hukumar, an kulle ofishohinsu, domin hana sace wasu takardu a hukumar.”

Olanipekun Olukoyede ya zama Sakataren hukumar EFCC ne watan Nuwamba 2018.

Saurari cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Online view pixel