Kano: Kotu ta garkame mutumin da ake zargi da yiwa wata yarinya ‘yar shekara 7 fyade

Kano: Kotu ta garkame mutumin da ake zargi da yiwa wata yarinya ‘yar shekara 7 fyade

A ranar Talata, wata kotun Majistare da ke Kano,ta ba da umarnin garkame wani mutum mai shekaru 55, Abdullahi Haladu, a gidan gyara hali na Goron Dutse, bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara 7 fyade.

Mutumin wanda ake zargi da aikata wannan mummunan laifi da ya saba wa sashe na 283 na final kot, mazauni ne a Unguwar Mahauta ta kauyen Gani da ke jihar Kano.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara, ASP Badamasi Gawuna, ya shaidawa kotun cewa, wani mutum mai suna Isa Uba, shi ne ya yi karar Haladu a ofishin 'yan sanda na Sumaila a ranar 29 ga watan Yuni.

Mallam Uba wanda shi ma mazauni ne a Unguwar Mahauta, ya yi ikirarin cewa, wanda ake zargi ya aikata laifin ne da misalin karfe 8.00 na dare, inda ya yi amfani da hikima wajen shigar da yarinyar dakinsa kuma ya aikata masha'a da ita.

Sufeto Janar na 'Yan sanda; Muhammad Adamu
Hoto daga jaridar Vanguard

Sufeto Janar na 'Yan sanda; Muhammad Adamu Hoto daga jaridar Vanguard
Source: Twitter

Alkalin kotun Muhammadu Idris, ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Agusta, inda ya ba da umarnin a yi wa Haladu tanadin matsugunni a gidan Dan Kande.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, mani mutum dan shekaru 48 mai suna Umaru Aliyu ya shiga hannun jami'an tsaro saboda lalata yarinya mai shekaru 3 da yayi.

Wanda ake zargin ya yi wa yarinyar fyade ne a wani tafki da ke kusa da gidansa a yankin Mararaba ta karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

KARANTA KUMA: A cikin shekaru biyar, Najeriya ta samu $206bn daga man fetur - OPEC

Al'amarin ya faru a ranar 26 ga watan Mayun 2020, a sabuwar kasuwar lemu da ke karamar hukumar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin a wata tattaunawa da yayi da Punch a Lafia.

Ya ce, "A ranar 27 ga watan Mayun 2020, an kai korafin wani Umaru Aliyu da ke sabuwar kasuwar 'yan lemu da ke karamar hukumar Karu.

"Ana zarginsa da lalata yarinya mai shekaru 3."

Kwamishinan ya kara da cewa, bayan samun rahoton, ya aika 'yan sanda kuma sun damko wanda ake zargin inda suka fara bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel