'Yan sanda sun damke dattijo mai shekaru 48 da ya yi wa yarinya fyade

'Yan sanda sun damke dattijo mai shekaru 48 da ya yi wa yarinya fyade

Wani mutum mai shekaru 48 mai suna Umaru Aliyu ya shiga hannun jami'an tsaro saboda lalata yarinya mai shekaru 3 da yayi.

Wanda ake zargin ya yi wa yarinyar fyade ne a wani tafki da ke kusa da gidansa a yankin Mararaba ta karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Al'amarin ya faru a ranar 26 ga watan Mayun 2020 a sabuwar kasuwar lemu da ke karamar hukumar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin a wata tattaunawa da yayi da Punch a Lafia. Ya ce tuni aka kama wanda ake zargin.

Ya ce, "A ranar 27 ga watan Mayun 2020, an kai korafin wani Umaru Aliyu da ke sabuwar kasuwar 'yan lemu da ke karamar hukumar Karu. Ana zarginsa da lalata yarinya mai shekaru 3."

'Yan sanda sun damke dattijo mai shekaru 48 da ya yi wa yarinya fyade

'Yan sanda sun damke dattijo mai shekaru 48 da ya yi wa yarinya fyade Hoto: Daily Trust
Source: Depositphotos

Kwamishinan ya kara da cewa, bayan samun rahoton, ya aika 'yan sanda kuma sun damko wanda ake zargin inda suka fara bincike.

KU KARANTA KUMA: Magu ya yi martani a kan 'ribar' saman N550bn da ake zarginsa da kwashewa

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da bayyana cewa jami'an sun damke wani mutum mai shekaru 42 mai suna Aliyu Adamu a kan lalata yarinya mai shekaru 8 da yayi yayin da take hanyar zuwa Islamiya.

Longe ya kara da cewa, al'amarin ya faru wurin karfe 6 na yamma a ranar 26 ga watan Mayun 2020, a garin Lafia.

Kamar yadda yace, a halin yanzu sashen binciken manyan laifuka ke duba al'amarin kafin su kai shi kotu.

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa tsoho dan shekara 60 mai suna, Mista Okafor Ndubuisi, ya shiga hannun ‘yan sanda kan zargin lalata ‘yar shekara 9.

Lamarin ya afku ne a karamar hukumar Oyi da ke jihar Anambra.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar wanda ake zargin ya sha lalata da yarinyar sau da dama a dakinsa.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Mohammed, ya ce yan sandan da ke aiki a sashin 3-3, Nkwelle Ezunaka a karamar hukumar Oyi, sun kama Okafor Ndubuisi kan zargin lalata yarinya yar shekara 9.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel