Da duminsa: Korona ta kara harbin yan Najeriya 571 yau
1 - tsawon mintuna
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 571 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.40 na daren ranar Lahadi 12 ga Yulin shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 571 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-152
Ebonyi-108
Edo-53
Ondo-46
FCT-38
Oyo-20
Kwara-19
Plateau-17
Osun-14
Bayelsa-14
Ekiti-14
Katsina-14
Akwa Ibom-11
Kaduna-11
Rivers-11
Niger-10
Ogun-7
Kano-6
Cross River-4
Bauchi-2
Jimillan wadanda suka kanu 32,558
Wadanda suka warke 13,447
Wadanda suka mutu 740
Asali: Legit.ng