'Na yi lalata da yaro ne saboda sha'awa ta takurani bayan na sha jike - jike' - Bello

'Na yi lalata da yaro ne saboda sha'awa ta takurani bayan na sha jike - jike' - Bello

Jami'an hukumar NSCDC sun kama wani matashi Yusuf Bello, mai shekaru 25, bisa zarginsa da aikata lalata da wani karamin yaro mai shekaru 11.

Jami'an tsaron sun kama matashin ne a garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Da ya ke jawabi ga manema labarai yayin bajakolin ma su laifi a hedikwatar rundunar, kwamandan NSCDC a jihar Nasarawa, Dakta Muhammad Mahmoud Fari, ya ce an kama Bello jim kadan bayan aikata laifin.

Da ya ke amsa laifinsa, Bello ya zargi wani maganin gargajiya da ya sha da tunzura shi wajen haikewa karamin yaron.

"Na sha wani maganin gargajiya kwanaki kadan bayan bikin Sallah karama, na karbi maganin ne a wajen wani mai magani bayan na fara gudawa.

"Ya siyar min da maganin a kan N150 kuma ya sanar da ni cewa bashi da wata illa, amma bayan wasu sa'o'i da shan maganin sai wata matsananciyar sha'awa ta takura min.

'Na yi lalata da yaro ne saboda sha'awa ta takurani bayan na sha jike - jike' - Bello

Jami'an NSCDC
Source: UGC

"Na kasa jure karfin sha'awar da ke damuna, shine na shiga bandaki, ina cikin bandakin ne sai yaron ya zo shi ma ya na son amfani da bandakin, shine na ce ya shigo kawai, na yi lalata da shi don samun saukin halin da nake ciki," a cewarsa.

DUBA WANNAN: 'Kisan girmamawa': Wani miji ya kashe matarsa ta hanyar jefeta da duwatsu

Dakta Fari ya ce daga cikin saura ma su laifin da su ka kama akwa wasu garada da su ka aikata laifin fyade ga wasu kananan yara mata ma su shekaru 7 da 7, da kuma wani mutum da ya dirkawa wata yarinya, mai shekaru 13, ciki.

A cewar Dakta Fari, yanzu haka yarinyar ta na dauke da juna biyu mai wata 7.

Kwamandan ya kara da cewa sauran ma su laifin da su ka kama sun hada da mutane 7 da ake zargi da aikata sata, wasu mutane biyu da ke satar kayan aikin titin jirgin kasa, da kuma wasu 'yan damfara ta yanar gizo.

Ya kara da cewa nan bada dadewa ba za su gurfanar da dukkan ma su laifin a gaban kotu domin su girbi abinda su ka shuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel