Na ji kamar in mutu lokacin zaman gida na kullen korona – Rahama Sadau

Na ji kamar in mutu lokacin zaman gida na kullen korona – Rahama Sadau

Jarumar Nollywood da Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana irin halin da ta shiga yayin da aka saka dokar kulle ta COVID-19.

"Irin rayuwar da na yi yayin kulle ba a cewa komai. Ina zaune wuri guda – na karanta latifai na gaji, na kalli fina finai na gaji, na yi hira da kawaye na gaji. Komai ya ginshe ni."

A hirar da ta yi da BBC Hausa a ranar Juma'a, Rahama ta ce ta yi wuyan gani ne saboda dokar lockdown da aka saka.

Na ji kamar in mutu lokacin zaman gidan na kullen korona – Rahama Sadau
Rahama Sadau. Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

"Rayuwar duk komai ya ginshe ni kuma na ji kamar zan mutu."

"... a sana'ar mu, muna yin abubuwa ne don mutane kuma idan ba ka samu ikon ganawa da mutane ba duk abin sai ya fita maka daga rai.

"Ina ganin annobar korona ta fi shafar masu sanaar fim."

Har ila yau, Jarumar ta yi magana kan rashin ganin ta da ba ayi a musamman a Kannywood inda ta ce makaranta ta koma.

DUBA WANNAN: Hotunan hatsabiban ƴan bindiga da sojoji suka kashe a Arufu

"Na tafi wata Jami'a a Cyprus inda na karanci Nazarin Kula da mutane kuma karatun ne ya sa ba ni da lokacin wasu abubuwa amma yanzu na gama kuma na fara aiki a kan wani abun."

Rahama ta kuma cewa akwai kyawawan maza da dama da ke suka rika neman ta aure su amma idan sun yi tambaya, "na kanyi murmushi na musu godiya kuma ina son kara jadada cewa ba ni da saurayi a Kannywood."

Ta kuma ce ba ta da raayin shiga siyasa a yanzu. "Bana sha'awar shiga siyasa a yanzu amma ban san ko zan canja ra'ayi nan gaba ba."

Rahama tana daga cikin jaruman Kannywood da suka tsinduma Nollywood ake dama wa da su kamar su Ali Nuhu, Yakubu Mohammed, Sani Danja, Usman Uzee da Maryam Booth.

Ta fito a fim din Nollywood mai suna ‘Sons of The Caliphate’. A Kannywood, Rahama ta fito a fina finai da dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel