Sarkin Kano ya bayyana matakin da zai dauka a kan fyade

Sarkin Kano ya bayyana matakin da zai dauka a kan fyade

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa, masarautarsa za ta hada kai da ma'aikatar kula da harkokin mata ta jihar Kano a yunkurinsa na yakar annobar fyade da ta fada jihar.

Ya sanar da hakan ne a yayin da kwamishinar harkokin mata ta jihar Kano, Malama Zahara'u Umar da tawagarta suka kai masa ziyara a fadarsa a ranar Alhamis.

Kamar yadda yace, matsalar fyade tana bukatar hadin kan kowa da kowa don dakileta gaba daya.

A bangaren Malama Zahara'u Umar, ta koka a kan yadda jama'a suke cewa a dinga rufa asirin mutanen da aka kama da aikata irin wannan laifin.

Ta kara da tabbatar da cewa, mutanen gari sun san masu tafka laifukan amma sai su dinga cewa a rufe maganar saboda ta cikin gida ce.

Sarkin Kano ya bayyana matakin da zai dauka a kan fyade

Sarkin Kano ya bayyana matakin da zai dauka a kan fyade. Hoto daga BBC
Source: UGC

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651

A wani labari na daban, daga yanzu rundunar 'yan sanda za ta fara gurfanar da duk wani mai kango a jihar Kano tare da duk wanda aka kama da laifin aikata fyade a cikin kangon da ya mallaka.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce rundunar 'yan sanda ta yanke wannan shawara ne bayan sakamakon rahoton bincike ya nuna cewa kaso 33.3 na laifin fyade ana aikata shi a cikin kangwayen jama'ar da ba a kammala ginasu ba.

"Bincikenmu ya nuna cewa kaso 33.3 na laifin fyade an aikatasu ne a cikin kango da ba a kammala gininsu ba, sannan an fi lalata kananan yara a irin wadannan wurare," a cewar Abdullahi.

Ya ce bayan fitowar sakamakon binciken ne rundunar 'yan sanda ta bullo da tsarin fadada sintirin da jami'anta ke yi zuwa kangwaye da ke lungun da sakon jihar Kano.

Rundunar 'yan sanda ta gargadi ma su kangwaye a jihar Kano su karasa ginasu domin kaucewa gurfana a gaban kotu da laifin taimakon ma su laifi, musamman aikata fyade a kan kananan yara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel