Matar da guntulewa mijinta Azzakari ta haihu, ta samu 'da namiji

Matar da guntulewa mijinta Azzakari ta haihu, ta samu 'da namiji

Halima Ali, matar da ta yankewa Mijinta, Aliyu Umar, al'aurarsa a jihar Taraba da samu karuwar 'da namiji a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, 2020.

A rahoton da Daily Trust ta samu, an garzaya da Halima asibitin Jalingo ne daga ofishin yan sanda ranar Laraba yayinda ta fara nakuda.

An tattaro cewa Halima da dan jinjirinta na cikin koshin lafiya kuma nan ba da dadewa ba za'a gurfanar da ita a kotu kan laifin azabtar da mutum da kuma kokarin kisa.

Yayinda aka bayyana Halima gaba manema labarai, ta ce ta yi nadamar abinda tayi.

DUBA WANNAN: Abubuwa 5 da suka faru da Ibrahim Magu cikin kwanaki 4

Matar da guntulewa mijinta Azzakari ta haihu, ta samu 'da namiji

Aliyu Umaru
Source: Twitter

A ranar Talata, 30 ga Yuni, 2020, uwargidar Aliyu Umaru, Halima, ta guntule masa azzakari da wuka.

Yana kwance yanzu a asibiti cikin radadin jiki da zuciya a asibitin koyarwan gwamnatin tarayya dake Gombe, inda aka kaisa bayan aukuwan hadarin.

A asibitin, an ga yadda Likitoci suka sanya masa na'ura na musamman domin taimaka masa wajen fitsari yayinda aka ajiye azzakarinsa da matar ta yanke gefe guda cikin leda.

A hirar da jaridar Punch tayi da shi, Aliyu Umar ya bayyana irin iftila'in ya shiga ciki.

Yace: "Ni dillalin Likitocin dabbobi ne. Ina sayar da magungunan dabbobi. shekaru na 42 kuma ina da mata biyu da yara biyu."

"Ni mazaunin garin Tella ne a karamar hukumar Gassol a jihar Taraba. An turo ni asibitin koyarwan tarayya Gombe ne daga FMC Taraba."

"Bayan dawowa na daga aiki, na debi ruwa don yin wanka kuma na ci abincin da iyalina ta girka kuma nayi bacci. Daga baya wani mugun azaba ya tasheni daga barci ina iwu."

"Uwargidata ta yanke min 'bura'. A lokaci aka sanar da makwabta. Ban sani ba (akwai yiwuwan) an sanya magani cikin abincin saboda yadda nayi bacci mai zurfi. Matata ta lalata min rayuwa kuma akwai takaici."

Rahotanni sun nuna cewa Halima ta kasance cikin takun tsaka da mijinta da kishiyarta.

Dan'uwan Umaru, Malam Usman ya bayyana cewa yana gidansa cikin dare aka kirashi a waya cewa akwai matsala.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel