Ana zargin wani tsoho da yaro da yi wa karamar yarinya fyade a Potiskum

Ana zargin wani tsoho da yaro da yi wa karamar yarinya fyade a Potiskum

Ana zargin cewa wani mutumi Baffa Ado mai shekaru 50 a Duniya da kuma Usman Musa Lampo, matashi ‘dan shekara 20 sun keta alfarmar wata karamar yarinya.

A ranar 8 ga watan Yuli, 2020, jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ana zargin wadannan mutane biyu da yi wa yarinya mai shekaru takwas a Duniya fyade a Yobe.

Kamar yadda mu ka samu labari, wannan mummunan abu ya faru ne a unguwar Bolewa, a karamar hukumar Potiskum da ke jihar Yobe.

Bala Tiyande wani daga cikin ‘yanuwan wannan yarinya, ya bayyanawa ‘yan jarida cewa an yi lalata da ita ne sa’ilin da aka aike ta zuwa debo ruwa a wata rijiya da ke gidan makwabta.

Wannan mummunan abu ya auku ne a wata Asabar, a ranar 27 ga watan Yuni, 2020.

“Yarinyar ta ce bayan ta gaza samun ruwa a gidan farko da aka aika ta, wani matashi ya sa karfi, ya kai ta cikin wani gida, ya yi amfani da ita.”

KU KARANTA: An kama mata da miji da bindigogi a jihar Kebbi

“Bayan tsawon lokaci ta fito daga gidanta, sai mahaifiyarmu ta rutsa ta da tambayoyi, da farko sai ta ki magana, amma da aka tursasa ta, ta bayyana abin da ya faru.”

“An kai maganar gaban ofishin dakarun NSCDC da ke Potiskum inda aka gudanar da bincike, sai yarinyar ta amsa cewa wani mutumi ‘dan shekara 50 ya dade ya na yin lalata da ita.”

Bayan samun wannan labari ne aka bada shawarar a kai maganar wajen ‘yan sanda domin ayi cikakken binciken da ya kamata.

Tiyande ya ce: “Bayan na fadawa jami’in NSCDC na garin Potiskum matsayarmu, sai ya ce ba zai iya mika mu ga 'yan sanda ba, ya bada shawarar mu rubuta takardar janye maganar, mu kuma nemi 'yan sanda su kama wanda ake zargi.”

Da aka tuntubi Kakakin NSCDC na jihar Yobe, ASC Bala Garba, ya musanya hakan, ya ce akwai matakan da ma’aikatansu ke bi wajen binciken zargi da laifin aikata fyade.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel