Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 503 sun kamu da cutar Koronan yau Talata
1 - tsawon mintuna
Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 503 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.40 na daren ranar Talata 7 ga Yulin shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 503 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;
Lagos-153
Ondo-76
Edo-54
FCT-41
Enugu-37
Rivers-30
Benue-24
Osun-20
Kaduna-15
Kwara-13
Abia-9
Borno-8
Plateau-6
Taraba-5
Ogun-3
Kano-3
Kebbi-2
Nasarawa-2
Bayelsa-1
Gombe-1
29,879 ne jimmilan wadanda suka kamu
12,108 aka sallama kawo yanzu
669 sun mutu
Asali: Legit.ng