Ba zamu kara baiwa masu fyade beli ba, muna shawarar fara dandankesu - El-Rufa'i

Ba zamu kara baiwa masu fyade beli ba, muna shawarar fara dandankesu - El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufa'i ya ce dokokin jihar ba zasu kara amincewa a baiwa masu laifin fyade beli ba.

Ya bayyana hakan ne yayinda wata kungiyar fafutuka na mata zalla suka kai masa ziyara gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim dake Kaduna ranar Litnin.

Gwamna ya bayyana cewa tuni jihar ta kafa dokar yaki da fyade, amma ana shirin sauye-sauye cikin dokar da zai bada damar dandake duk wanda aka kama da laifin.

Yace: "Na ji dadi shugaban Alkalan jihar ya yanke shawarar daukar mataki mai tsauri kan lamarin."

"Mu kanmu muna kokari kuma mun san wannan fitinar fyaden zai zama tarihi."

"Idan mutum ya yiwa mace babba fyade shekaru 21 zai yi a kurkuku amma idan karamar yarinya ce daurin rai da rai za'ayi masa."

"Bayan daurin shekaru 21 kuma, duk wanda kotu ta kama da laifin fyade za'a cire masa azzakari saboda idan ya fito daga Kurkuku, ba zai sake iya yiwa wata fyade ba."

"Muddin azzakarin na jikinsa, akwai yiwuwan zai sake komawa gidan jiya."

"Yawancin masu aikata wannan laifi matasa ne, saboda haka bayan shekaru 21, za su iya komawa su cigaba."

Ba zamu kara baiwa masu fyade beli ba, muna shawarar fara dandankesu - El-Rufa'i

El-Rufa'i
Source: Facebook

Ya kara da cewa tuni yan majalisar dokokin jihar sun shirya dokar dandakewa kuma ya yi alkawarin gwamnati za ta dau mataki.

"Ana bukatan irin wannan matakin saboda ba a samun nasarar damke masu fyade sakamakon hana yan matan zuwa shaida kotu saboda kunyar da iyaye keyi da kuma gudun isgilin al'umma.

"Mun bayyana karara cewa zamu boye fuskokin wadanda aka yiwa fyade. Saboda haka babu wani matsala zuwa shaida kotu. Za suyi shaida a bayan fagge, babu wanda zai gan ki ko fuskarki." El-Rufai yace.

Gwamnan ya yi kira ga iyaye su yiwa yaransu tarbiyya tare da baiwa yara mata hakkinsu da ya kamacesu. NAN ta ruwaito.

Mai magana da yawun kungiyar, Saratu AbdulAziz, ta ce sun zo gidan gwamnatin ne domin neman taimakon gwamnan wajen ganin an kawo karshen yawan fyade a jihar.

A bangare guda, za ku tuna cewa mambobin majalisar dattawa sun yi watsi da shawarar fidiye masu fyade matsayin ukuba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel