Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Magu, shugaban EFCC

Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Magu, shugaban EFCC

Hukumar 'yan sandan fararen kaya (DSS) ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

An damkesa ne bayan kwanaki kadan da Abubakar Malami, antoni janar kuma ministan shari'ar Najeriya ya zargesa da almundahana.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, shugaban EFCC ya yi tafiya zuwa birnin Dubai da ke daular larabawa ba tare da sanin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kuma a yayin kullen kasa.

A lokacin da aka tuhumesa, ya ce ya je wani bincike ne. Ana zargin shugaban da rayuwar da ta fi abinda yake samu daga aikinsa.

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng