Jami'an tsaro sun damke daliban firamare da sakandare 35 a liyafar dare, an samu kwaroron roba

Jami'an tsaro sun damke daliban firamare da sakandare 35 a liyafar dare, an samu kwaroron roba

A samamen da 'yan sandan kasar Kenya su ka kai wani gidan haya da ke jerin rukunin gidajen haya da ke Sango, a birnin Homa Bay a ranar Juma'a, sun kama dalibai 35 na firamare da sakandire.

A yayin da 6 suka tsere, yara mata 20 da maza 15 masu shekaru 13 zuwa 17 sun shiga hannu bayan sun yi mankas da giya kuma tsirara, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

An samu kwaroron roba da aka yi amfani da su a dakunan baccin gidan. Shugaban 'yan sandan yankin, Robert Lango ne ya jagoranci sauran jami'an inda suka damke yaran 'yan makaranta.

Lango ya ce wasu iyaye ne suka karbar wa 'ya'yansu biyu mata hayar gidan, amma sai makwabta suka sanar da hakan bayan jin sauti mai amo.

An damke mamallakin gidan mai suna Patrick Ayieko.

Ya ce: "Mun samu kwaroron roba da aka yi amfani dasu wanda muka sakankance cewa yaran ne suka yi lalata. Shida daga cikinsu sun tsere bayan isarmu.

“Wasu daga cikin kananan yaran suna saka kaya lokacin da muka isa. Sun mayar da gidan tamkar mashaya.

“Na kira tawagata inda muka isa gidan. Muka kulle kofa sannan 'yan sandan suka iso a ababen hawa tare da damke yaran.

"An kama mamallakin gidan mai suna Patrick Ayieko a kan barin yaran da yayi suna rashin da'a a cikin gidansa."

An kwashe dukkansu zuwa ofishin 'yan sanda da ke Home Bay amma an sake su daga baya saboda rashin wurin ajiyesu.

Kwamandan 'yan sandan yankin Homa Bay, Sammay Koskey, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an kira iyayen yaran kuma za su hallara a ofishin 'yan sandan a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Jami'an tsaro sun damke daliban firamare da sakandare 35 a liyafar dare, an samu kwaroron roba

Jami'an tsaro sun damke daliban firamare da sakandare 35 a liyafar dare, an samu kwaroron roba. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum 544 sun sake kamuwa da korona, jimillar ta hararo 29,000

A wani labari na daban, wata mata 'yar asalin Florida mai suna Kris Hedstrom ta maka makwabcinta a kotu tare da bukatar sanin mahaifin akuyoyinta biyar da ta siya a watan Disambar da ta gabata.

Karar da Hedstrom ta cike na bukatar kodai Heather Dayner ya dawo mata da $900 wanda ta biya don siyan wadannan akuyoyin Najeriya a Disamba, ko kuma a yi gwajin kwayar halittar akuyoyin don gano tsatsonsu.

A karar da ta shigar, ta ce tayi tsammanin za ta iya yi wa akuyoyinta rijista ne a kungiyar akuyoyin kasar Amurka.

Hedstorm ta ce: "Dayner, mamallakin gidan gonar Baxter da ke Odessa ya sanar da ni cewa uban akuyoyin yana da rijista a kungiyar amma kuma kungiyar ta ki karbar akuyoyin saboda banbancinsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel