A fuska ya ke jefa min kororon roba idan ya dawo lalata da ƴan mata - Mata ta fadawa kotu

A fuska ya ke jefa min kororon roba idan ya dawo lalata da ƴan mata - Mata ta fadawa kotu

Wata matar yar kasar Zambia mai shekara 60 ta shaidawa kotu cewa za ta yi sulhu da mijinta mai shekara 89 ne idan ya amince ya yi gwajin kwayar cutar HIV.

A cewar matar, mijinta ya kan jefe ta da kororon roba da ya yi amfani da shi tare da yan matarsa duk lokacin da ya dawo daga yin lalata da su kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ta ce, "Miji na mai shekara 89 ya kan jefa min kwaroron robar da su kayi amfani da yan matansa a fuskta ta kuma ya ce min ba ni da amfani."

A cewar Zambia Observer, matar mai suna Astridah Bwale ta bayyana cewa mijinta mai shekara 89, Rodrick Mwale ya fada mata cewa wari ta ke yi kuma akwai matan da suka fi da kyau a waje.

Miji na ya kan jefe ni da kororon robar da su kayi amfani da shi da yan matarsa

Miji na ya kan jefe ni da kororon robar da su kayi amfani da shi da yan matarsa. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: An yi wa wani jirgin UN ruwan harsashi a Borno

Ta shaidawa kotu cewa ba ta taba ganin albashin mijinta ba kuma baya sayan abinci a gidan don iyalansa su ci.

Astridah ta yi ikirarin cewa yan matansa ne kawai ke cin kudin Rodrick.

Wacce ta shigar da karar ta ce mijinta ya karbu allawus dinsa na sallama daga aiki ba tare da ta sani ba kuma ba ta san abinda ya aikata da kudin ba.

Ta kuma yi korafin cewa a cikin shekaru hudu da suka gabata, Rodrick baya kwana a gidansa, ya tare a gidan budurwarsa hakan yasa ba su kwanciya irin ta aure.

Har wa yau, ta shaida wa kotu cewa gidan da suke zaune da iyalanta babu rufi domin wanda aka yi karar ya ki siyan rufin gida.

Ta shaidawa kotu cewa za ta yi sulhu da mijinta mai shekara 89 idan har ya amince zai yi gwajin kwayar cutar HIV.

Ma'auratan sun da ke da yara tara sun fara samun matsala ne tun a 1988 bayan mijinta ya samu aiki.

Da ya ke bayar da baasi, Rodrick ya shaidawa kotu cewa sun fara samun matsala ne a shekarar 2015 bayan matarsa ta dena wanke masa kaya.

Ya kuma shaidawa kotu cewa matarsa ta dena ba shi hakkinsa na kwanciyar aure kuma rabonsa da kwanciya tare tun shekarar 2015.

Shugaban kotun Nsama Banda ya yi sulhunta ma'auratan kuma ya umurci su tafi suyi gwajin cutar HIV.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel