Yadda jami'an NCDC sukayi rikici da wani mai Korona da akayi kokarin kaiwa cibiyar killacewa (Bidiyo)

Yadda jami'an NCDC sukayi rikici da wani mai Korona da akayi kokarin kaiwa cibiyar killacewa (Bidiyo)

Wani faifan bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jami'an hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC suka fafata da wani mutum da gwaji ya nun ya kamu da cutar Coronavirus.

Jami'an hukumar sun garzayo gidan mutumin ne domin kaishi cibiyar killace masu cutar domin jinya amma yace sam ba zai je ba.

Sai jami'an suka fara fizgarshi karfi da yaji suna kokarin fitar dashi daga gidansa sai an tafi shi yayinda shi kuma yana dura musu ashar, yana iwun cewa ba ya son tafiya da su.

Jami'an dai suka yi kunne kashi suna cigaba da fizgar sa.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel