Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ebonyi ya kamu da cutar Coronavirus
1 - tsawon mintuna
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kamu da muguwar cutar nan ta Coronavirus.
Gwamnan ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki da safiyar nan.
Ya ce shi da wasu hadimansa sun kamu da cutar sakamakon gwajin da sukayi.
Ya kara da cewa a yanzu haka babu wani alaman rashin lafiya tattare da su amma tuni sun killace kansu bisa sharrudan da hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta gindaya.
Gwamnan ya umurci mataimakinsa, Kelechi Igwe, ya hau ragamar mulki da cigaba da kula da yadda jihar ke yaki da cutar domin kare rayukan al'ummar jihar.
Umahi ya yi kira mutan jihar su dau umurci hukumar NCDC da gaske.

Asali: UGC
Saurari cikakken rahoton...
Asali: Legit.ng