Dandake masu fyade: Naziru Sarkin waka ya yi wa El-Rufai martani mai zafi

Dandake masu fyade: Naziru Sarkin waka ya yi wa El-Rufai martani mai zafi

Fitaccen mawaki Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka, ya yi wa Gwamna Nasir El-Rufai martani a kan cire mazakutar masu fyade matukar aka kama su da laifin hakan.

A makon da ya gabata ne BBC ta ruwaito wani rahoto mai cewa, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nemi da a dinga yi wa masu fyade dandaka.

Kamar yadda rahoto ya zo: "Gwamnan jihar Kaduna ya ce babbar hanyar magance matsalar fyade da ta addabi al'umma shine yi wa masu aikata laifin dandaka.

"Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka yi da shi ta manhajar Zoom a ranar Asabar.

"An yi taron ne da nufin samo hanyar magance matsalar fyade da ta ci ta ki cinyewa a kasar nan.

"A cikin harshen turanci, gwamnan ya ce "Remove the tools" wanda ke nufi a cire kayan aikin."

Gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna, an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 a cikin kankanin lokaci, alkalumma ne suka nuna.

Sai dai Naziru Sarkin waka ya soki wannan ra'ayin na gwamnan inda ya nuna sam bai kamata hakan na fitowa daga bakin mutum kamar sa ba.

Dandake masu fyade: Naziru Sarkin waka ya yi wa El-Rufai martani mai zafi

Dandake masu fyade: Naziru Sarkin waka ya yi wa El-Rufai martani mai zafi. Hoto daga The Punch
Source: UGC

KU KARANTA: Yadda wani mutum ya dirkawa yarinya ciki, ya jefar jaririn a daji

A shafinsa na Intagram, ya wallafa cewa, "Idan mazakuta ake nufi, wannan bai dace ya fito daga bakin wanda ya san Allah ba.

"Kuma addinin Musulunci bai bada wannan damar ba, hasalima duk dokokin duniya basu bada wannan damar ba.

"Duk tausayinka ga bawa, baka kai mahaliccinsa ba kuma duk son ka da gyara baka kai Manzon Allah SAW ba, amma bai ce a yi hakan ba.

"Kana so ka ce ka fi Allah da Annabinsa sanin mai ya kamata ne? Kamata yayi ka kaddamar da shari'ar Musulunci a garinka, shine za mu san kana son a yi gyara.

"Amma ana shaye-shaye, ana shirka kuma ana yawo tsirara duk bamu gyara ba, toh meye zai gyaru? Mu bi Allah kawai shine za mu ga dai-dai. Allah yasa mu dace Ameen.

"Ku sani, babu wanda yafi karfin zuciyarsa sai wanda Allah ya so."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel