UN ta dakatar da ma'aikatanta 2 a kan bidiyon lalatarsu da ya bazu

UN ta dakatar da ma'aikatanta 2 a kan bidiyon lalatarsu da ya bazu

Majalisar dinkin duniya ta sanar da dakatar da ma'aikatanta biyu da ke cikin bidiyon batsa a kasar Isra'ila, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Mai magana da yawun sakataren majalisar, Stephane Dujarric ya bayyana hakan ga manema labarai a New York a ranar Alhamis.

Dujarric ya ce an gano ma'aikatan kuma an dakatar da su ba tare da biyan albashi ba har zuwa lokacin da za a kammala binciken zargin da ake musu.

Wani bidiyo ya karade kafafen sada zumuntar zamani a makon da ya gabata wanda ke nuna namiji da mace a mazaunin motar majalisar suna jima'i a Tel Aviv.

A ranar Juma'a, Dujarric ya sanar da manema labarai cewa majalisar ta matukar firgita kuma ta damu da bidiyon don haka ta fara bincike a kai.

Ya tabbatar da cewa an nadi bidiyon ne a wajen motar kuma akwai ma'aikatan majalisar ne na Truce Supervision Organisation (UNTSO) wacce ke da hedkwata a birnin Qudus.

Gajeren bidiyon ya bayyana wata mace farar fata sanye da riga mai launin ja a cikin farar mota kirar SUV dauke da tambarin majalisar dinkin duniya.

UN ta dakatar da ma'aikatanta 2 a kan bidiyon lalatarsu da ya bazu

UN ta dakatar da ma'aikatanta 2 a kan bidiyon lalatarsu da ya bazu. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Tumbur: Bidiyon fasto yana kokarin lalata da matar aure

A tare da su a motar akwai direba da kuma wani mutum mai saiko da ke zaune a mazaunin fasinja a gaba.

Rahoton masu yada labarai ya nuna cewa, an nadi bidiyon a titin HaYarkon da ke Tel Aviv, babban birnin kasar Isra'ila.

Kakakin majalisar dinkin duniyar ya ce ofishin bincike na cikin gida na majalisar ke gudanar da binciken.

Ya ce: "An gano ma'aikata biyu na majalisar da ke cikin abun hawan a Tel Aviv wanda ake rashin da'a.

"Sakamakon zargin da ake musu na take dokar da'a a matsayinsu na ma'aikatanmu, an dakatar da su babu biyan albashi."

"Wannan dakatarwar za ta yi tasiri ne har sai an kammala bincike a kan abinda ake zargin su a kai. Za a ci gaba da binciken har zuwa kammalarsa kafin mu sanar da halin da ake ciki," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel