Tumbur: Bidiyon fasto yana kokarin lalata da matar aure

Tumbur: Bidiyon fasto yana kokarin lalata da matar aure

- Wani bidiyo mai cike da abun kunya da takaici ya fada kafafen sada zumuntar zamani

- A bidiyon, an ga faston ya yi tumbur inda yake kokarin lalata da matar aure a dakin mijinta

- Ta yaudaresa ya cire kaya kafin ta bar jama'a su shigo don ganinsa tare da tozartar shi

Wani bidiyo mai matukar bada mamaki da takaici ya shiga kafafen sada zumuntar zamani. A bidiyon, an ga faston na kokarin lalata da matar auren a cikin gidan mijinta.

Matar ta biye masa inda ta barshi ya tube kaya duka kafin ta bude kofar mijinta da wasu su shigo don tozarta shi.

A bidiyon, an ga faston tsirara yana neman gafara a kan guiwoyinsa tare da bukatar kada su fallasa shi.

Amma kuma matar da yake yunkurin lalata da ita, ta sha alwashin kiran matarsa don ta ganewa idonta abun kunyar da mijinta yayi.

KU KARANTA: Ango ya rasu bayan shafawa sama da 'yan biki 100 cutar korona

A wani labari na daban, a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2020, dan fashi da makami mai suna Adeniyi Ajayi, ya bayyana cewa matan aure da 'yan aiki yake wa fyade a kan idon mazansu don hakan ya zama ladabtarwa idan aka hana shi kudi yayin da yaje fashi da makami.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Adeniyi ya shiga hannun jami'an runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami ta jihar Legas. Sun kama shi a wani otel da ke yankin Ijora 7-up a jihar.

Adeniyi wanda ke fashi da makaminsa shi kadai, ya addabi jama'ar Sabo, Ijora Badia da sauransu.

A lokacin da aka bayyana cewa an kama shi, mata takwas wadanda suka hada da ma'aikatan gwamnati da lauyoyi sun isa ofishin SARS don tabbatar da cewa ya yi musu fyade bayan fashi da makami da yayi.

'Yan mata biyu da ke aiki a wani kamfani a Sabo, sun ziyarci ofishin SARS inda suka bayyana yadda wanda ake zargin ya yi musu fyade a gaban abokan aikinsu maza, da rana tsaka a ranar 16 ga watan Yunin 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel