An gurfanar da madugun mai fyade a Kano bayan ya yi wa tsohuwa mai shekaru 85 fyade

An gurfanar da madugun mai fyade a Kano bayan ya yi wa tsohuwa mai shekaru 85 fyade

- Wani matashi mai shekaru 32, Mohammed Zulfaralu, ya gurfana a gaban wata babbar kotun majiatare da ke zama a Kano kan zargin yi wa tsohuwa yar shekaru 85 fyade

- Ana kuma tuhumar matashin da yunkurin yi wa matan aure uku fyade bayan ya haura gidansu

- Dan tsohuwar da ya yi wa fyade da mazajen matan da ya yi yunkurin lalata da su ne suka kai karansa ofishin yan sanda

An gurfanar da wani matashi mai shekaru 32, Mohammed Zulfaralu, a gaban wata babbar kotun majiatare da ke zama a Kano kan zargin yi wa tsohuwa yar shekaru 85 fyade.

An gurfanar da matashin ne a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli.

Wanda ake karan, Zulfaralu, wanda ke zaune a Gidan Kwana, kauyen Kwanar Dangora, yana kuma fuskantar tuhuma na yunkurin yi wa matan aure uku fyade.

An gurfanar da madugun mai fyade a Kano bayan ya yi wa tsohuwa mai shekaru 85 fyade

An gurfanar da madugun mai fyade a Kano bayan ya yi wa tsohuwa mai shekaru 85 fyade Hoto: Thisdaylive
Source: UGC

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Badamasi Gawuna ya fada ma kotun cewa wani Abubakar Yusuf na Kwanan Dangora, a ranar 8 ga watan Yuni, ya kai karan mai laifin zuwa ofishin yan sanda bayan ya yi lalata da tsohuwa mai shekaru 85.

Ya yi zargin cewa wani lokaci a watan Nuwamban 2019, wanda ake karan ya shiga gidan mahaifiyar mai karan da ke Unguwar Rimi na Kwanar Dangora, sannan ya yi mata fyade.

Dan sandan ya kara da cewa laifin ya ci karo da sashi na 344 da 283 na dokar.

Gawuna ya fada ma kotun cewa wanda ake karan ya yi yunkurin yi wa matan aure uku fyade.

Ya ce mazajen matan sun kai kara ofishin yan sandan Kwanar Dangora a ranar 5 ga watan Yuni, cewa mai laifin ya haura gidajensu sannan ya yi yunkurin yi masu fyade.

Gawuna ya lissafa sunayen masu korafin a matsayin Hamza Shuaibu, Yusuf Sani da Sani Samaila.

Sai dai wanda ake karan ya amsa laifin tuhumar da ake masa.

KU KARANTA KUMA: Wani kwamishina a jihar Plateau ya kamu da cutar korona

Alkalin da ya jagoranci shari’an, Muhammad Idris, ya umurci yan sandan da su gabatar da jawabin wanda ake karan.

Daga bisani Idris, ya yi umurnin rufe wanda ake karan a gidan kurkuku inda ya dage shari’an zuwa ranar 20 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel