Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu (Hotuna)

Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu (Hotuna)

Wata mata mai shekaru 28 a kasar India ta haifa jaririya da bata da kafa da hannuwa a kauyen Sakla da ke Sironj Tehsil a yankin Vidisha, rahotanni daga yankin sun nuna.

A bidiyon da ya bayyana, an ga wata mata rike da jaririya ba hannuwa da kafafu a cikin bargo.

Dr Suresh Aggarwal, likitar yara ce da ke aiki a asibitin Rajiv Gandhi Smriti da ke Sironj. Ta ce jaririyar na cike da koshin lafiya.

Amma kuma likitoci sun yanke shawarar kara duba lafiyar jinjirar don samun tabbacin cewa komai na jikinta na aiki daidai.

Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu

Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu. Hoto daga The Nation
Source: UGC

Ciwon da ke damunta ana kiransa da Tetra-Amelia Syndrome wanda ke faruwa bayan sauyawa a kwayar halitttar WNT3 wanda ba a cika samu ba.

DUBA WANNAN: Mata mai juna biyu ta datse mazakutar mijinta da wuka a Taraba

Kamar yadda shugabar Bhopal CMHO da kuma likitan Dr Prabhakar Tiwari suka bayyana, ana iya samun jinjiri daya a cikin 100,000 mai irin wannan nakasar.

Ta ce wannan ne karo na farko da ta gani a tsayin lokacin da ta diba tana aiki.

A 2011, wani bincike da Dr Eva Bermejo-Sanchez na cibiyar bincike da ke kasar Spain ya ce, ana samun irin wannan nakasar ne a jinjiri daya tak cikin 71,000.

Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu

Iko sai Allah: An haifa jinjira babu hannuwa da kafafu. Hoto daga The Nation
Source: UGC

Mahaifiyar na da cikin jinjirar na watanni biyar yayin da hoto ya nuna cewa hannuwa da kafafu basu girma.

Bayan shawarar da aka bata na zubar da cikin, matar da saurayinta sun yanke shawarar cewa suna son su haifi jinjirar yadda ta ke.

A shekarar 1982, an haifa Nicholas James Vujicic da irin wannan nakasar.

A halin yanzu, ya yi aure har ya haifa 'ya'ya hudu kuma fitaccen marubuci ne.

Ya ziyarci a kalla kasashe 44 a fadin duniya.

A yayin zantawa da manema labarai a wata hirar awa daya da aka yi da matarsa mai suna Kanae, ta bayyana yadda ake tsangwamarsa a lokacin suna kanana don ya taba yunkurin kashe kansa lokacin yana da shekaru 10.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel