An damke Fasto mai shekaru 54 ya yiwa 'yar 12 fyade

An damke Fasto mai shekaru 54 ya yiwa 'yar 12 fyade

Hukumar yan sanda a jihar Ogun sun damke wani Fasto mai suna, Niyi Omowodun, da laifin yiwawtaa yar shekara 12 fyade a garin Itele-Ota, karamar hukumar Ado Odo/Ota ta jihar, DT ta ruwaito.

Faston, wanda mazaunin Ejigun Agbede Itele Ota ne ya shiga hannun hukuma bayan mahaifin yarinyar ya shigar da kara ofishin yan sandan Itele.

Wakilin DT ya tattaro cewa mahaifin ya bayyanawa jami'an yan sanda cewa ya samu kira a wayar tarho daga daya daga cikin makwabtansa cewa an zakkewa 'yarsa.

A cewarsa, Faston makwabcinsu ne kuma aka damkeshi yana kan lalata da ita.

Jawabin da kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya saki ranar Laraba ya nuna cewa bayan samin rahoton, DPO na Itele, Monday Unigbe, ya tura jami'ansa suka damke Faston.

Oyeyemi ya ce Faston wanda ya kasance shugaban cocin Helmet of Life International Church, Itele – Ota, ya amsa laifin yiwa yarinyar fyade.

Yace: "Yayinda bincike, mutumin wanda yayi ikirarin cewa shi faston cocin Helmet of Life International Church, Itele – Ota, ne ya amsa laifin lalata yarinyar."

"Ya kara da cewa ya ja hankalin yarinyar zuwa cikin wani kango dake unguwar yayinda aka tura ta aike. Yayinda aka tambayeshi ko yana da mata, mutumin ya ce ya rabu da matarsa tun shekarar 2016."

Ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya bada umurnin mayar da lamarin sashen safara da cin zarafin yara domin cigaba da bincike da kuma gurfanar da shi.

KU KARANTA: Gwamnan Plateau, Simon Lalong, ya shiga killace kansa bayan kwamishanansa ya kamu da cutar Korona

An damke Fasto mai shekaru 54 ya yiwa 'yar 12 fyade

An damke Fasto mai shekaru 54 ya yiwa 'yar 12 fyade
Source: Facebook

omin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel