Kaduna: An tsinci gawar yarinya mai shekaru 6 da aka yi wa fyade a masallaci

Kaduna: An tsinci gawar yarinya mai shekaru 6 da aka yi wa fyade a masallaci

- An tsinci gawar wata karamar yarinya 'yar shekaru 6 da ake zargin anyi mata fyade har ta mutu a cikin wani masallaci da ke jihar Kaduna

- Lamarin ya afku ne a ranar Juma'a a yayinda aka bude masallacin da misalin karfe 3:00 na rana

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce suna gudanar da bincike

An tsinci gawar wata yarinya 'yar shekaru 6 da ake zargin anyi mata fyade har ta mutu a cikin wani masallaci da ke Sabon titi, a Kurmin Mashi ta wurin Nnamdi Azikiwe bypass da ke karamar hukumar Kaduna ta arewa a jihar Kaduna.

Daily Trust ta gano cewa al'amarin da ya faru a ranar Juma'a ya janyo hankalin masu jaje da suka hada da jama'ar yankin.

Sai da masu jaje suka yi tsaye a kan al'amarin kafin iyayen yarinyar su amince a kaita asibitin kwararru don dubata.

Kaduna: An tsinci gawar yarinya mai shekaru 6 da aka yi wa fyade a masallaci

Kaduna: An tsinci gawar yarinya mai shekaru 6 da aka yi wa fyade a masallaci Hoto: The CCable
Source: UGC

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce, "duk da har yanzu ba a kama kowa ba, amma jami'an 'yan sanda na Kurmin Mashi sun fara bincikar mummunan al'amarin.

" Tabbas an kawo rahoton al'amarin ofishin 'yan sanda da ke Kurmin Mashi a ranar Juma'a. Jami'an mu sun amsa kira daga jama'ar Kurmin Mashi bayan sun samu gawa a cikin masallaci.

"Saboda dokar hana walwalwa, basu bude masallatai sai a ranakun Juma'a. Sun samu gawar wurin karfe 3:20 na rana.

KU KARANTA KUMA: Uwargidar marigayi Ajimobi da mataimakin gwamnan jihar Oyo sun yi musayar kalamai (bidiyo)

"An fara bincike a kan al'amarin duk da har yanzu ba a kama kowa ba. Amma jami'an mu suna kan al'amarin don gano tushensa. Idan an kama wani, zan sanar daku."

A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ta gurfanar da wani Tela mai shekaru 27 mai suna Taiwo Odetunde a gaban wata kotun majistare da ke Ado-Ekiti.

An zargi telan da jan yara mata biyu masu shekaru 13 da 14 inda ya yaudaresu da alkawarin cewa zai dinka musu takunkumin fuska sannan yayi musu fyade.

'Yar sanda mai gabatar da kara, Monica Ikebuilo, ta sanar da kotun cewa wanda ake karar na fuskantar zargi a kan fyade kuma ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Yunin 2020 a Ado-Ekiti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel