Talla ke sa ana yi wa kananan yara fyade - Kwamishinan 'yan sanda

Talla ke sa ana yi wa kananan yara fyade - Kwamishinan 'yan sanda

Kwamishinan 'yan sandan jihar Bauchi, Lawan Jimeta, a ranar Alhamis ya bai wa iyaye shawara a kan yadda suke barin yaransu mata suna talla, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce hakan ke sa ana yi musu fyade tare da duk wani nau'in cin zarafi da yara mata ke fuskanta.

Jimeta ya bada wannan shawarar ne a taron wata kungiya mai zaman kanta mai suna muryar mata da shugabanci, wacce ta kai masa ziyara a Bauchi.

Kwamishinan ya ce talla ga yara mata babban hatsari ne kuma hakan ne ke sa ana yi musu fyade tare da duk wani nau'in cin zarafi.

"Iyaye da masu kula da yara nake shawarta da su kiyaye dorawa yaransu mata talla," Jimeta yace yayin da yake jawabi a kan yadda matsalar fyade ke ci gaba da yawaita.

Ya yi kira ga kungiyoyin taimakon kai da kai da su dage wurin wayar da kan jama'a a kan cin zarafin yara da kuma hanyar dakile shi a jihar da kasa baki daya.

Kwamishinan ya bada tabbacin cewa rundunarsa za ta sa jami'an kula da cin zarafin jinsi wajen tabbatar da sun karba dukkan korafin da ya shafi jinsi a jihar da karfi.

Ya kara da kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su shirya tarukan wayar da kai tare da bayyana hadurran cin zarafin jinsi.

Talla ke sa ana yi wa kananan yara fyade - Kwamishinan 'yan sanda

Talla ke sa ana yi wa kananan yara fyade - Kwamishinan 'yan sanda. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Magani a gonar yaro: Magungunan cutuka 7 da Zobo ke yi ga dan Adam

Tun farko, shugabar kungiyar, Comfort Attah, ta nemi tallafi da goyon bayan kwamishinan 'yan sandan wurin yaki da cin zarafin mata da kananan yara.

Hakazalika, yayin taron, wata 'yar kungiyar mai suna Maryam Garba ta yi bayanin cewa ayyukan kungiyar ya shafi kananan hukumomi 11 da ke fadin jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, kungiyar muryar mata da shugabanci ta kunshi kungiyoyin mata na taimakon kai da kai da suka hada daa gidauniyar ASHH, Rahama, FOMWAN da FAHIMTA.

Tun bayan saka dokar kulle a kasar nan, an fuskanci yawaitar fyade ga kananan yara da kuma 'yan mata a sassan kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel