Yanzu-yanzu: Buhari ya amince da Victor Giadom matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar APC

Yanzu-yanzu: Buhari ya amince da Victor Giadom matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da mataimakin sakataren jam'iyyar All Progressives Congress APC, Victor Giadom, a matsayin sahihin mukaddashin shugaban uwar jam'iyyar.

Legit Hausa ta samu labarin hakan daga mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu.

Garba Shehu ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin Laraba, 24 ga Yuni, 2020.

Malam Garba yace: "Shugaban kasa ya samu gamsasshen shawarar doka kan halin da jam'iyyar ke ciki kuma ya gano cewa doka ta nuna cewa Victor Giadom ne mukaddashin shugaban uwar jam'iyya."

"Kuma saboda shi mai biyayya ga doka ne, shugaban kasa zai halarci taron majalisar zartaswar jam'iyyar da Giadom ya shirya ta yanar gizo gobe da rana."

"Hakazalika, banda shugaban kasa, wasu gwamnoni da shugabannin majalisar dokokin tarayya zasu halarta."

Yanzu-yanzu: Buhari ya amince da Victor Giadom matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar APC
Yanzu-yanzu: Buhari ya amince da Victor Giadom matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar APC
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel