Yadda matashi ya yi wa kanwarsa mai shekaru 5 fyade ta mutu

Yadda matashi ya yi wa kanwarsa mai shekaru 5 fyade ta mutu

Wata mata da danta sun shiga hannun 'yan sanda bayan danta ya yi wa 'ya'yan kanwarta biyu da take riko fyade. Hakan yayi sanadiyyar mutuwar karamar mai shekaru biyar.

Khadijah M. Saccoh da yayarta na zama tare da yayar mahaifiyarsu tare da danta a garin Freetown, da ke Sierra Leone.

Iyayen Khadijah sun rabu da juna amma mahaifinta na zama a Amurka don a can aka haifi yaran. Ya so tafiya da yaran amma alkali ya hana shi saboda mahaifiyarsu bata amince ba.

Khadijah da yayarta suna tare da yayar mahaifiyarsu ne a kasar Sierra Leone.

Amma kuma, dan yayar mahaifiyarsu ya fara yi wa yayar Khadijah fyade mai shekaru 8, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifiyar dan ta gane fyaden da yayi amma sai ta boyewa iyayen yaran tare da jinyar yarinyar.

Dan ta ya koma inda ya yi wa Khadijah fyade amma sai ta boye tare da kokarin jinyarta. Cike da tsautsayi Khadija ta ce ga garinku amma sai marikiyarta ta yi yunkurin gaggauta birneta.

Yadda matashi ya yi kanwarsa mai shekaru 5 fyade ta mutu

Yadda matashi ya yi kanwarsa mai shekaru 5 fyade ta mutu Hoto: Linda Ikeji
Source: UGC

Kamar yadda rahotanni suka nuna, ta sanar da 'yan uwan mahaifin Khadija tare da bukatar birneta. Tuni mahaifin yace yana son sanin abinda ya kashe diyarsa.

Ya bai wa 'yan uwansa umarnin daukar gawar yarinyar tare da mika ta asibiti don bincike.

Bincike ya nuna cewa fyade aka yi wa yarinyar ba sau daya ba, hakan ne ya zama silar ajalinta.

A take mahaifin ya bukaci a kai babbar asibiti don dubawa, lamarin da yasa aka gano cewa an yi mata fyade ita ma.

DUBA WANNAN: Damfarar da sunan matar marigayi Abba Kyari: Rundunar 'yan sanda ta kama Aminu Ado

A halin yanzu 'yan sanda sun kama yayar mahaifiyar Khadija da danta kuma ana bincike a kansu kafin a mika su kotu.

A wani labarin kuma, rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke Yusuf Saleh mai shekaru 36 sakamakon zarginsa da ake da yin luwadi da kaninsa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ahmed Wakili, wanda ya bayyana hakan a wata takarda, ya ce an kai musu rahoton al'amarin a ranar 5 ga watan Afirilun 2020. Kuma mahaifin yaran ne ya kai rahoton.

Ya ce Saleh ya ja kaninsa zuwa wani kango inda ya yi lalata da shi ta baya.

DSP Wakili ya kara da cewa, wanda ake zargin ya siyawa wanda ya lalata biskit da lemun kwalba don toshe masa baki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel