An ci moriyar ganga: 'Yadda 'yan damfara suka tura wa karuwai 'alert' din bogi bayan gama lalata

An ci moriyar ganga: 'Yadda 'yan damfara suka tura wa karuwai 'alert' din bogi bayan gama lalata

Rundunar 'yan sanda babban birnin tarayya da ke Abuja ta damke wasu mutum 24 da ake zargin su da laifukan da suka hada da amfani da sakon banki na bogi wurin biyan kayan da suka siya tare da biyan karuwan da suka yi lalata da su.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Frank Mba, ya ja hankalin mutane da su gane cewa ana amfani da sakon banki na bogi wurin siyan kaya da damfarar mutane.

Kamar yadda yace, an kama kashi na farko na masu laifin wadanda suka kware a tura sakon bogi na kudi daga banki ga wadanda suka damfara.

Ya ce an kama su ne bayan sun biya wasu karuwai da wannan sakon bogin.

Amma kuma, ya yi kira ga jama'a da su kiyaye da yadda jama'a ke zuwa siyan kaya sannan su ce za su biya ta yanar gizo.

Shugaban kungiyar 'yan ta'addan wanda ya zanta da manema labarai a kan ayyukan kungiyar, ya tabbatar da cewa wannan sakon bankin na daukan mintuna kalilan ne kafin ya bace daga waya.

Mba ya kara da cewa sun kama wasu 'yan uwa uku wadanda suka kware da damfarar jama'a. Suna karbar tallafi daga jama'a da sunan gidauniyar Frank Mba don yaki da annobar korona.

An ci moriyar ganga: 'Yadda 'yan damfara suka tura wa karuwai 'alert' din bogi bayan gama lalata

An ci moriyar ganga: 'Yadda 'yan damfara suka tura wa karuwai 'alert' din bogi bayan gama lalata. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Mutum 675 sun sake kamuwa da korona, jimilla ta kai 20,919

A wani labarii na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wasu ma'aurata bayan matar mai suna Tomisin Onyeokweni ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara a gaban mijin mai suna Osas Onyeokweni.

Ma'auratan sun yaudari budurwar mai shekaru 20 zuwa wani kango kafin matar da ke dauke da almakashi ta yaga mata riga tare da barinta tsirara. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin.

Oyeyemi ya ce matar ta saka kwalba a gaban tsohuwar budurwar mijinta amma da taimakon mijin nata.

Oyeyemi ya ce, budurwar ta samu wannan tsinuwar tare da tozarcin ne saboda ta taba soyayya da mijin matar kafin su yi aure.

Kakakin rundunar 'yan sanda ya kara da cewa an kama ma'auratan bayan wacce abun ya faru da ita ta kai rahoto zuwa ofishin 'yan sanda da ke Agbara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel