Yadda matar aure ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara tare da tura mata kwalba a gaba

Yadda matar aure ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara tare da tura mata kwalba a gaba

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wasu ma'aurata bayan matar mai suna Tomisin Onyeokweni ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara a gaban mijin mai suna Osas Onyeokweni.

Ma'auratan sun yaudari budurwar mai shekaru 20 zuwa wani kango kafin matar da ke dauke da almakashi ta yaga mata riga tare da barinta tsirara.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin.

Oyeyemi ya ce matar ta saka kwalba a gaban tsohuwar budurwar mijinta amma da taimakon mijin nata.

Oyeyemi ya ce, budurwar ta samu wannan tsinuwar tare da tozarcin ne saboda ta taba soyayya da mijin matar kafin su yi aure.

Kakakin rundunar 'yan sanda ya kara da cewa an kama ma'auratan bayan wacce abun ya faru da ita ta kai rahoto zuwa ofishin 'yan sanda da ke Agbara.

Ta ce tsohon saurayintta mai suna Osas ne ya kirata a waya tare da bukatar ta samesa a kusa da yankin Lusada don wata muhimmiyyar magana da za su yi.

Ya kara da cewa, ma'auratan sun dauko hoton budurwar tsirara tare da barazanar baza shi a yanar gizo matukar ta kai rahoton al'amarin.

Yadda matar aure ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara tare da tura mata kwalba a gaba

Yadda matar aure ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara tare da tura mata kwalba a gaba. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Ku zage damtse, ko mu saita muku hanya - Lawan ga Shugabannin tsaro

Oyeyemi ya ce, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu amma sun yi matukar nadamar abinda suka yi.

Ya ce, "An kama ma'auratan bayan korafin da budurwar ta kai ofishin 'yan sanda da ke Agbara. Ta ce tsohon saurayinta Osas wanda yanzu ya aura kawarta, ya kirata a waya da ta samesa a yankin Lusada don wani muhimmin zance.

"Ta kara da cewa, ta sameshi tare da matarsa inda suka ja ta wani kango. A nan matar ta yi amfani da almakashi ta farke mata riga tare da yi mata tsirara.

"Bayan yi mata tsirara, Osas ya riketa yayin da matarsa ta tura mata kwalba a gabanta. Sun kuma dauka hotunanta tsirarar tare da yin barazanar sakinsa a yanar gizo matukar ta kai rahoto."

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce an damke ma'auratan sannan sun amsa laifinsu tare da nuna nadamar yin hakan.

Amma kuma kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson ya bada umarnin mika wadanda ake zargin gaban kotu bayan kammala bincike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel