Mataimakin shugaban jami'ar BUK, Farfesa Wakili, ya rasu
Allah ya yi wa Farfesa Haruna Wakili rasuwa, kamar yadda sanarwa da safiyar ranar Asabar ta bayyana.
Marigayi Farfesa Wakili ya kasance mataimakin shugaban jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), wato DVC (Deputy Vice Chancellor) mai kula da sha'anin gudanarwa.
A baya, marigayi Wakili ya taba rike mukamin kwamishinan ilimi a jihar Jigawa a tsohuwar gwamnatin PDP.
Ba a bayyana sanadiyyar mutuwarsa ba.

Asali: Twitter
Marigayi Wakila Farfesa ne a bangaren ilimin tarihi (History).
DUBA WANNAN: An kori janar a rundunar sojin Najeriya 'babu girma, babu arziki'
Jami'ar BUK ta yi rashin manyan Farfesoshi a 'yan kwanakin baya bayan nan sakamakon barkewar annobar yawaitar mace - macen jama'a a jihar Kano.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng