Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara (Hotuna)

Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara (Hotuna)

Kabilar Kambari mutane ne da suka dade a yankunan karkara na jihar Neja. Suna kadan daga cikin mutanen da ke rayuwa da tsiraici.

Kabilar Kambari na alfaharin zaman kansu ba tare da sun dogara da gwamnati ba.

An fi samun kabilar Kambari a Birnin Amina da ke karamar hukumar Rijau ta jihar Neja inda suke yawo tsirara. Kabila ce da aka manta da ita kuma suka gamsu da yanayin rayuwarsu tare da dogaro da kai ba tare da damuwa da gwamnati ba.

Jama'ar kabilar Kambari ba su yaren Hausa ko Turanci. Sunan yaren da suke yi Kambari. Suna zama a karamin yankin da suke kuma suna ma'amala da juna ne idan za su je gona ko kasuwa.

Sun gaji al'adar zama tsirara ne tun kaka da kakanni kuma wani abu ne da basu da niyyar dainawa.

Amma kuma idan suka tafi kasuwa siyar da hajojinsu, matan kan saka zani su rufe rabin jikinsu ta kasa, hakazalika mazan.

Jaki ne ya zamana abinda ke kai kawo da jama'ar kabilar Kambari.

Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara

Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara. Hoto daga The Pulse
Source: Twitter

A kabilar Kambari, ana yanka akuyoyi da shanu don yin abincin bikin aure yayin da iyayen amarya ke ciyar da dangin ango.

Bayan kammala cin abincin, hakan na nuna an daura aure.

Kamar yadda suke, abinda ke jan hankalin namiji ga mace ba tsiraici bane, yadda macen ta yi kitso, ladabinta da kuma tsagen jikinta ne.

KU KARANTA: Handama: EFCC ta gurfanar da mataimakin kakakin majalisa da magatakarda

Jama'ar kabilar Kambari ba Musulmi bane ko Kiristoci kamar yadda sauran 'yan arewacin Najeriya. Suna bautar Ubangijinsu na daban da suke kira da Magiro. Hakazalika, sun yadda da maita tare da tsafe-tsafe.

Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara

Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara. Hoto daga The Pulse
Source: Twitter

Kamar yadda aka sanar a baya cewa karamar hukumar Rijau suke, jama'ar kabilar Kambari manoma ne. Su ke samar da yawancin abincin da jama'ar yankin ke ci.

Sanannun amfanin gonar da suka fi nomawa sun hada da masara, dawa, wake da shinkafa.

Kusan dukkan jama'ar kabilar Kambari na kiwon kaji da akuyoyi don nama yayin da masu kudi daga cikinsu ke kiwon Shanu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel