Baturiya ta haifa jinjiri baƙi, ta daura laifi a kan mijinta

Baturiya ta haifa jinjiri baƙi, ta daura laifi a kan mijinta

- Dimuwa da rudani ya biyo bayan soyayyar da wani miji ya nuna wa matarsa har ya zauna da ita a asibiti yayin nakuda

- Fitowar jinjirin ke da wuya baturiyar kasar Spain ta ganshi baki, lamarin da yasa ta zargin mijinta da cin amanarta tare da lalata da bakaken fata

- Duk da mijin ya musanta aukuwar lamarin, matar ta ce tabbas ta kama shi yana hira a yanar gizo da wata mata bakar fata

Al'amarin ya faru a wani asibitin kasar Spain a ranar Litinin. Baturiyar tana nakuda a asibiti tare da mijinta.

Komai na tafiya daidai kafin jaririn ya bayyana, lamarin da ya kawo tashin hankali da dimuwa.

Da farko likitocin sun yi tsammanin ciwo ne yasa jinjirin yayi baki amma daga baya sai aka gano cewa lafiyarsa kalau amma baki ne.

Bayan wahalar nakudar, mahaifiyar ta bude hannu don karbar jinjirin amma sai ta ga abun mamaki.

Tuni ta fara ihu da tsawa ga maigidanta. "Kai mugu, na san kana cin amanata. Kalla abinda kayi. Bace min daga idona!"

Mahaifiyar bata yi kasa da gwiwa ba ta fashe da kuka. Lamarin da yasa mijin ya tsaya tamkar bishiya.

Baturiya ta haifa jinjiri baki, ta zargin mijinta da lalata da bakake

Baturiya ta haifa jinjiri baki, ta zargin mijinta da lalata da bakake. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mahaifin mai neman takarar gwamna a Edo a APC

Masana kiwon lafiyar sun mutunta bukatar matar inda suka bukaci maigidan da ya fice yayin da suke rike dariyarsu.

Bayan kwanaki biyu, magidancin ya zanta da manema labarai. "Ina ta kokarin yi mata magana amma ta ki saurarata. Ni kuwa bana son bata mata rai.

"Dole ne in rungumi zargin da ake min."

Daga bangaren mai jegon kuwa, "Likitoci sun ce hakan ba zai yuwu ba amma na taba kama shi yana hira ta yanar gizo da bakar mace."

A wani labari na daban, wasu kananan yara biyu da ba a ambaci sunansu ba sun rasa rayyukansu a ranar Laraba bayan gini ya rufta a kansu a Gafari Balogun na Ogudu da ke jihar Legas.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce ginin ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai karfi. Ya kara da cewa wadanda suka mutu kananan yara ne kuma an ciro gawarwakinsu daga baraguzan ginin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel