Yadda kawa ta kai kawarta wurin mutum 8 suka yi mata fyade

Yadda kawa ta kai kawarta wurin mutum 8 suka yi mata fyade

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta damke wata mata mai shekaru 30 mai suna Zainab Jafaru, wacce ke daya daga cikin mutum tara da suka yi wa kawarta mai shekaru 33 fyade a Yola, babban birnin jihar.

An zargi Zainab da yaudarar kawarta inda ta kaita maboyar masu fyaden.

'Yan sandan sun ce sun kama mutum biyar daga cikinsu yayin da hudu har yanzu ake kan nemansu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ce Zainab ta yaudari kawarta inda ta kaita wurin maza tara suka yi mata fyade sannan ta tsere.

Yadda kawa ta kai kawarta wurin mutum 8 suka yi mata fyade

Yadda kawa ta kai kawarta wurin mutum 8 suka yi mata fyade Hoto: Premium Times
Source: Depositphotos

Nguroje yace: "A ranar 13 ga watan Yunin 2020, mun samu rahoto daga wata budurwa mai shekaru 33 wacce ta ce masu fyade tara sun yi lalata da ita a Gerio, kauyen Jambutu da ke karamar hukumar Yola ta arewa.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Akwai yuwuwar mu sake garkame Kaduna - El-Rufai

"Tuni muka tura jami'an rundunar inda suka damko Ahmadu Ismail mai shekaru 20, Salu Buba mai shekaru 25, Mohammed Ali mai shekaru 78, Abubakar Ali mai shekaru 28 sai Zainab Jafaru mai shekaru 30.

"Lamarin ya faru a ranar 12 ga watan Yuni inda Zainab Jafaru ta yaudari wacce ta kawo kara a kan ta raka ta wurin saurayinta.

"Bayan isarsu, saurayin Zainab wanda har yanzu ba a kama ba ya kira abokansa wadanda suka yi wa mai korafin fyade."

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa wani Alkalin kotun majistare da ke zama a Makurdi ya bukaci a adana masu wani dan achaba mai shekaru 28 a kan zarginsa da lalata yarinya mai shekaru 6 a duniya.

Al'amarin ya faru a kauyen Idye da ke Makurdi a jihar Binuwai.

Kotun ta gano cewa wanda ake zargin mai suna Terver Awuha da ke kauyen Idye a Makurdi ya lalata yarinyar har sau biyu.

Dan sanda mai gabatar da kara ya sanar da kotun cewa, a ranar 5 ga watan Yunin 2020, mahaifiyar yarinyar mai suna Deborah Omachi ta kai kara ofishin 'yan sandan yankin.

Ta ce a ranar 3 ga watan Yuni wurin karfe 7:30 na yammaci, ta aika diyarta siyo taliya. Yayin da take kan hanya, wanda ake zargin ya ja yarinyar da karfi zuwa cikin dakinsa inda yayi lalata da ita.

Ta kara da cewa, a ranar 5 ga watan Yuni, wanda ake zargin ya sake jan yarinyar wurin karfe 2 na rana inda yayi lalata da ita tare da bata N100.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel