Rundunar 'yan sanda ta bayyana wurin da aka fi aikata fyade a Kano

Rundunar 'yan sanda ta bayyana wurin da aka fi aikata fyade a Kano

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce daga cikin laifukan fyade 42 da aka kai mata rahoton faruwarsu a tsakanin watan Janairu zuwa Mayu na shekarar 2020, an aikata mafi yawan laifin ne a kango.

Abdullahi Haruna, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, ne ya sanar da hakan yayin tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Alhamis.

Kakakin ya bayyana cewa sun gurfanar da dukkan wadanda ake zargi da aikata fyade a gaban kotu.

Ya bayyana cewa alkaluma sun nuna cewa an aikata kaso 33.3% na laifin fyade a cikin kango daban - daban a sassan Kano, yayin da aka aikata kaso 17.7 a gonaki da ke wajen gari.

"An aikata kaso 15.6% na laifin fyade a cikin shaguna, kaso 15.6 a gidajen masu laifin, kaso 8.9 a makarantu, kaso 6.7 a gidajen wadanda aka yi wa fyaden da kuma kaso 2.2 a kasuwanni," a cewar Haruna.

Sannan ya kara da cewa, "rundunar 'yan sanda ta na iya bakin kokarinta wajen daukan mataki a kan laifukan fyade da sauran laifuka da suka shafi cin zarafin mata da kananan yara."

Rundunar 'yan sanda ta bayyana wurin da aka fi aikata fyade a Kano

'Yan sanda
Source: UGC

Kazalika, Haruna ya bayyana cewa an samu raguwar yawaitar aikata fyade a jihar Kano idan aka kwatanta da alkaluman da aka samu a kwatankwacin irin wannan lokaci a shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Daukan sabbin ma'aikata: Babban kwamandan NSCDC ya bayyana halin da ake ciki

Haruna ya bukaci jama'a su hanzarta sanar da rundunar 'yan sanda a duk lokacin da suka samu wani da laifin aikata fyade ko cin zarafin mata da kananan yara domin gaggauta daukan mataki.

"Yin shiru ba tare da an sanar da rundunar 'yan sanda ba, zai bawa masu laifin karfin gwuiwar sake aikata laifin.

"Kofofinmu a bude suke domin karbar shawarwari, musamman a irin wannan lokaci na bukatar kowa ya zama mai sa ido, rundunar 'yan sanda a shirye take ta yi aiki da jama'a domin warware matsalolin da suke damunsu," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel