Alkali ya bai wa dan achaba masauki a gidan yari a kan laifin lalata karamar yarinya

Alkali ya bai wa dan achaba masauki a gidan yari a kan laifin lalata karamar yarinya

Wani Alkalin kotun majistare da ke zama a Makurdi ya bukaci a adana masu wani dan achaba mai shekaru 28 a kan zarginsa da lalata yarinya mai shekaru 6 a duniya.

Al'amarin ya faru a kauyen Idye da ke Makurdi a jihar Binuwai.

Kotun ta gano cewa wanda ake zargin mai suna Terver Awuha da ke kauyen Idye a Makurdi yayi lalata da yarinyar har sau biyu.

Dan sanda mai gabatar da kara ya sanar da kotun cewa, a ranar 5 ga watan Yunin 2020, mahaifiyar yarinyar mai suna Deborah Omachi ta kai kara ofishin 'yan sandan yankin.

Alkali ya bai wa dan achaba masauki a gidan yari a kan laifin lalata karamar yarinya

Alkali ya bai wa dan achaba masauki a gidan yari a kan laifin lalata karamar yarinya Hoto: Thisdaylive
Source: UGC

Ta ce a ranar 3 ga watan Yuni wurin karfe 7:30 na yammaci, ta aika diyarta siyo taliya. Yayin da take kan hanya, wanda ake zargin ya ja yarinyar da karfi zuwa cikin dakinsa inda yayi lalata da ita.

Ta kara da cewa, a ranar 5 ga watan Yuni, wanda ake zargin ya sake jan yarinyar wurin karfe 2 na rana inda yayi lalata da ita tare da bata N100.

Mai gabatar da karar ya kara da cewa, dan achabar ya aikata laifin da ya ci karo da sashi na 284 na Penal Code na 2004.

A saboda haka, Alkalin bai saurari rokon da aka yi masa ba. A take ya bukaci a adana masa wanda ake zargin a gidan gyaran hali a Makurdi.

KU KARANTA KUMA: Kunyi kasa a gwiwa, ba zan sake daukan wani uzuri ba - Buhari ga Hafsoshin tsaro

Alkali Isaac Ajim ya dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Augusta.

A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa Pauline Tallen, Ministar kula sa harkokin mata ta Najeriya ta alakanta hauhawar fyade da dokar kulle da aka saka don dakile yaduwar annobar korona a Najeriya.

Tallen ta sanar da hakan ne ga manema labaran gidan gwamnati a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2020 bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya inda ta kawo matsalar fyade gabansu.

Ta bayyana cewa za a dauki mataki wanda zai hada da na shari'a da kuma kafafen yada labarai don shawo kan matsalar fyade.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel