Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu rahotannin fyade 42 a cikin wata 5

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu rahotannin fyade 42 a cikin wata 5

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta samu rahotannin fyade 42 a fadin jihar tsakani watan Janairu zuwa watan Mayun 2020.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Alhamis a Kano.

Haruna ya bayyana cewa rundunar ta bincike rahotannin fyade 42 cikin watannin biyar kuma na mika wadanda ake zargi gaban kotu.

Ya ce kiyasin da aka yi, kashi 33.3 na fyaden duk da aka yi a jihar an yi su ne a kangon gine-gine yayin da kashi 17.7 an yi su ne a gonaki.

"Kashi 15.6 an aikata su a shago, kasi 15.6 an aikata a gidajen wadanda ake zargin, kashi 8.9 an yi a makarantu, yayin da kashi 6.7 da kashi 2.2 aka aikata a kasuwanni da gidajen wadanda abun ya faru da su.

"Yan sanda na iyakar kokarinsu wurin daukar rahotan fyade da muhimmanci tare da duk wani cin zarafi da ya jibanci jinsi a jihar," yace.

Haruna ya kara da cewa yawan yadda ake fyade ya matukar raguwa a jihar idan aka danganta shi da na shekarar da ta gabata.

Yayin kira ga mazauna jihar da su garzaya don kai rahoton duk wani nau'i na cin zarafi, Haruna ya jaddada cewa rundunar sai ta ga karshen al'amarin.

Kakakin ya kara da cewa: "Yin shiru ba tare da kai rahoton fyade ba zai kara wa masu yi karfin guiwar aikatawa ne.

"Kofofinmu a bude suke don shawarwari a wannan lokacin na 'yan sandan jihar, rundunar ta mayar da hankali wurin dakile dukkan matsalolin al'umma."

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu rahotannin fyade 42 a cikin wata 5

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu rahotannin fyade 42 a cikin wata 5. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Yadda za a shawo kan matsalar 'yan bindiga a Katsina - Shugaban manoma

A wani labari na daban, matashiya mai shekaru 19 a yankin Ndola da ke Zambia ta tsere daga gidan mijinta saboda tsananin bukatar jima'i da mijinta ke yi wanda hakan ke zarcewa tsawon dare.

Matar auren da ke Mushili, ta yi bayanin hakan a gaban wata kotu da ke Kabushi. Ta ce ta tsere daga gidan mijinta saboda ya fiye bukata.

Yana ji mata ciwo kuma baya gamsuwa da wuri. Bata bacci don sukan kwashe tsawon dare suna aiki daya.

Charity ta ce mijinta na kwanciya da ita duk dare sannan yana bukatar samfur kala-kala. Hatta lokutan da take al'ada baya sassauta mata.

Ta yi bayanin cewa ba za ta iya jure irin wannan rayuwar ba da zai dinga kwanciya da ita kowacce rana, don haka ta tsere don neman mafita.

An mika shari'ar gaban Majistare Angnes Muswema wacce ke zaman kotun tare da Mildred Namwizye da Evelyn Nalwizya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel