Masoya biyu sun mutu yayin da su ke jima'i na 'kece raini' a otel

Masoya biyu sun mutu yayin da su ke jima'i na 'kece raini' a otel

Wasu dalibai a kwallejin fasaha da ke Nekede a garin Owerri na jihar Imo sun mutu yayin gasar yin lalata.

Daliban, Cynthia Obieshi da Samuel Osuji sun mutu ne a ranar Lahadi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar, Orlando Okeokwu ya ce an kai gawarwakin daliban asibiti don ajiye wa a dakin adana gawarwaki.

Wasu dalibai biyu sun mutu yayin gasar lalata a otel

Wasu dalibai biyu sun mutu yayin gasar lalata a otel. Hoto daga The Nation
Source: UGC

DUBA WANNAN: 'Da yardarsu muke saduwa', inji magidancin da ke zina da 'ya'yansa mata biyu

Ya ce, "A ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni ta 2020 bayan samun rahoto jami'an 'yan sanda da ke Hedkwatan Rundunar da ke Nekede/Ihiagwa, sun tafi daki mai lamba 19, a Vic-Mic Lodge da ke JMJ Bus stop.

"Sun kutsa cikin dakin inda suka tsinci gawarwakin wata Cynthia Obieshi da Samuel Osuji.

"An gano cewa ita Cynthia ta ziyarci saurayinta, Samuel a ranar 13 ga watan Yunin 2020 inda ta kwana tare da shi amma da gari ya waye dukkansu ba su farka ba.

"Binciken da kwararru suka fara gudanarwa ya nuna akwai yiwuwar sun mutu ne sakamakon kwayoyi da suka sha.

"A halin yanzu dai an kai gawarwarkinsu dakin ajiyar gawa yayin da ake cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin."

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa Adejare Adebisi, mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya rasu.

A cewar Ismail Omipidan, babban sakataren watsa labarai na gwamnan da ya fitar da sanarwar ta shafin Twitter na gwamnatin jihar, Adesibi ya rasu ne a daren ranar Juma'a bayan gajeruwar rashin lafiya.

Gwamnatin jihar ta ce mutuwar Adebisi ba ta da alaka da annobar COVID-19.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 54 a duniya.

Omipidan ya ce, "Ya rasu a daren jiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, mutuwarsa ba ta da alaka da annobar COVID-19.

"Za ayi jana'izar Adebisi a safiyar yau a garin Illobu a jihar Osun."

Gwamnan ya mika sakon ta'aziya ga iyalan mamacin inda ya ce mutuwar Adebisi babban rashi na a gare shi.

Ya ce, "Labarin rasuwarsa mataimakin shugaban ma'aikatan fada na, Jare Adebisi ya kada ni." "Rasuwarsa babban rashi ne gare ni da mutanen Illobu da jihar baki daya.

"Amma a matsayin mu na musulmi, mun rungumi kaddara tare da gode wa Allah cewa marigayin ya yi rayuwa ta gari.

"Ina mika ta'aziya ta ga daukakin iyalansa, jamiyyar APC, 'yan siyasa, gwamnati da jihar baki daya. Za muyi kewarsa sosai. Ina adduar Allah ya saka masa da Aljanna Firdausi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel