Yanzu-yanzu: Dan majalisa ya kamu da COVID-19

Yanzu-yanzu: Dan majalisa ya kamu da COVID-19

Dan majalissa mai wakiltar yankin Toro/Jama'a a Jihar Bauchi, Hon.Tukur Ibrahim ya kamu da muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau coronavirus.

Shugaban majalissar, Abubakar Suleiman ne ya bayyana hakan yayinda yan majalissar suka koma kan aiki a ranar Litinin.

Yace Ibrahim yana samun kulawa a daya daga cikin cibiyar killacewa a Jihar.

Ya kara da cewa an amshi samfurin wasu daga cikin mambobin domin ayi musu gwaji ya kuma shawarci sauran mambobin da su je suma ayi musu gwajin.

Suleiman yayi adduar Allah ya bashi Lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel