Matsalar fyade na matukar tada min hankali - Buhari

Matsalar fyade na matukar tada min hankali - Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari ya ce yana matukar fusata da annobar fyade da ta kunno kai a Najeriya.

Ya sanar da hakan ne a yayin jawabin ranar damokaradiyya na 2020 a yau Juma'a. Ya ce mulkinsa ya shirya yaki da cin zarafin jinsi ta duk hanyar da ta dace.

Ya ce, "Matan Najeriya har yanzu suna da matukar muhimmanci don haka dole ne a basu matsayi na alfarma a al'amuran kasar nan.

"Ina jinjinawa kwarin guiwarku da jajircewarku tare da gudumawar da kuke badawa wurin habakar kasar nan.

"Ina sanar da dukkan matan da ke fadin kasar nan cewa za mu kawo karshen cin zarafi na jinsi ta hanyar kafa dokoki da kuma wayar da kai.

"Na matukar fusata a kan yadda ake ta yi wa mata fyade da kananan yara. 'Yan sanda na kan al'amarin da kuma tabbacin za a damko masu laifi tare da ladabtar da su."

Ana ta zanga-zanga a fadin kasar nan bayan yawaitar fyade ga mata da kananan yara.

Vera Omozuwa budurwa ce mai shekaru 22 wacce aka yi wa fyade tare da kasheta a wata coci da ke Benin City.

Barakat Bello budurwa ce mai shekaru 18 da aka yi wa fyade tare da sassarata a garin Ibadan da ke jihar Oyo.

Matsalar fyade na matukar tada min hankali - Buhari

Matsalar fyade na matukar tada min hankali - Buhari. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

KU KARANTA: Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya aminta da shirye-shiryen da ma'aikatar kula da harkokin mata ta fitar don shawo kan matsalar fyaden kananan yara da mata a kasar nan.

Ministar kula da harkokin mata, Pauline Tallen, yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron yanar gizo da suka gama na majalisar zartarwa, ta ce ta mika bukatar daukar mataki a kan 'annobar fyade' gaban Buhari.

Tallen, wacce ta tabbatar da cewa bukatar ta samu goyon baya daga shugaban kasa, ta ce ma'aikatarta za ta tsaurara wayar da kai ta kafofin yada labarai tare da hadin guiwa da ma'aikatar yada labarai.

Ministar ta kwatanta yawaitar fyade a fadin kasar nan da abun kunya tare da kira ga jihohi da kada su sassauta wa masu fyade ko kadan.

Ta ce a cikin jihohi 36 na kasar nan, tara ne kadai ke amfani da dokar yaki da cin zarafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel