Garkuwa da mutane, fyade da kisa: Katsinawa sun sake fitowa zanga-zanga (Hotuna)

Garkuwa da mutane, fyade da kisa: Katsinawa sun sake fitowa zanga-zanga (Hotuna)

- Jama'ar jihar Katsina na ci gaba da zama cikin tsananin firgici da alhini sakamakon al'amuran 'yan bindiga

- A yau Alhamis, 11 ga watan Yunin 2020, mazauna kauyen 'Yan Kara sun fito don nuna damuwarsu ga gwamnati

- Jama'ar sun rufe manyan hanyoyi yayin zanga-zanga, lamarin da ya kawo tsananin cunkoson ababen hawa

Jama'ar jihar Katsina na ci gaba da zanga-zanga sakamakon al'amuran rashin tsaro da suka addabi jihar.

Mazauna kauyen 'yan kara da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun rufe manyan hanyoyi tare da kiran dauki daga gwamnati.

Sun zargi gwamnati da nuna halin ko in kula a kan fyade, kashe-kashe da garkuwa da mutane da 'yan bindiga ke yi a yankunan.

Al'amarin ya kawo tsananin cunkoso wanda ya hana masu ababen hawa wucewa a kan babbar hanyar.

Garkuwa da mutane, fyade da kisa: Katsinawa sun sake fitowa zanga-zanga (Hotuna)

Garkuwa da mutane, fyade da kisa: Katsinawa sun sake fitowa zanga-zanga (Hotuna). Hoto daga HumAngle
Source: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta

Garkuwa da mutane, fyade da kisa: Katsinawa sun sake fitowa zanga-zanga (Hotuna)

Garkuwa da mutane, fyade da kisa: Katsinawa sun sake fitowa zanga-zanga (Hotuna). Hoto daga HumAngle
Source: Twitter

Matasan sun dinga yawo da rubutu a manyan fostoci tare da rera wakoki inda suke bukatar kara tsananta tsaro a jihar.

Masu ababen hawa sun dinga sauya hanya sakamakon rufe hanyar da fusatattun matasan suka yi.

Wannan zanga-zangar ta fara ne bayan sa'o'i 24 da 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Faskari tare da halaka a kalla jama'a 40.

A yayin da aka tuntubi DSP Gambo Isah, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya ce ba zai iya tsokaci a kan lamarin ba saboda bincikar al'amarin.

"Ban san abinda zan ce a kan wannan al'amari ba. Muna bincike a kan al'amarin don haka ba za mu iya cewa komai ba sai jami'ai sun kawo rahoton abinda suka gano," ya sanar da The Cable.

Kafin harin kwanan nan, masu zanga-zangar sun cika titin garin Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina don neman karin tsaro.

Sun kone babbar fosta mai dauke da hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da logon APC.

Gwamnan jihar Katsina, ya sanar da cewa mulkinsa ya fara neman sulhu da 'yan bindiga.

Amma duk da hakan, 'yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare, lamarin da yasa Gwamna Masari ya yi nadamar neman sulhun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel