Da ɗumi-ɗumi: Gwamnoni sun saka dokar ta ɓaci a kan fyaɗe

Da ɗumi-ɗumi: Gwamnoni sun saka dokar ta ɓaci a kan fyaɗe

Kungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, ta amince da saka dokar ta baci a kan fyade, cin zarafin mata da kananan yara a Najeriya.

Sun kuma sake jaddada anniyarsu na ganin cewa dukkan wadanda aka samu da aikata wannan laifi sun fuskanci hukuncin da ya dace da su.

Hakan na cikin sakon bayan taro ne mai dauke da sa hannun shugaban NGF, Dr Kayode Fayemi bayan taro karo na 10 da kungiyar ta yi a kan COVID-19 ta intanet a ranar Laraba.

Gwamnoni sun saka dokar ta baci game da fyade

Gwamnoni sun saka dokar ta baci game da fyade. Hoto daga The Punch
Source: UGC

DUBA WANNAN: Buhari ya sha alwashin daukar babban mataki a kan masu fyade

An fitar da sakon bayan taron ne a Abuja a ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnonin sun amince da saka, "Dokar ta baci a kan fyade da cin zarafin mata. Gwamnonin sunyi tir da dukkan wani naui na cin zarafin mata da yara kanana sun dau aniyar ganin an hukunta wadanda aka samu da laifin.

"Ana kira ga gwamnonin da ba su riga sun amince da fara amfani da dokar hana cin zarafin mata da yara ba su gaggauta yin hakan tare da dokar da aka yi wa kwaskwarima na ganin an gurfanar da wadanda aka samu da laifin cikin gaggawa.

"Har wa yau dokar ta tanadi bude rajista na mutanen da aka samu da laifin yin fyade a kowanne jiha domin yi musu fallasa da kunyata su."

A wani rahoton, kun ji cewa babban kotu da ke zamanta a Igobosere, Legas a ranar Laraba ta yanke wa wasu maza biyu, Williams Udoh da Ubong Isiah hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An kuma yanke wa Udoh hukuncin shekaru 21 a gidan yari saboda yi wa matan aure fyade.

A Kano, yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 30 da aka ce ya yi wa kimanin mata 40 fyade a gari daya cikin shekara guda.

Kakakin yan sanda, Abdullahi Haruna ya tabbatar da kama wanda ake zargin inda ya ce wanda ake zargin, Mohammed ya amsa lafinsa.

Ya ce wadanda ya yi wa fyaden sun hada da yan mata, matan aure da tsofaffi.

Haruna ya ce wanda ake zargin ya shiga wani gida domin yi wa wata yarinya fyade ne amma mahaifiyarta ta yi ihu kuma hakan ya yi sanadin kama shi.

Nan ba da dade wa ba za a gurfanar da shi, in ji Haruna.

Yan sanda a jihar Benue a ranar Laraba sun kama wani likita da ake zargin ya yi wa yarinya mai shekara 11 fyade a Otukpo.

The Nation ta ruwaito cewa an dako yarinyar ne daga kauye domin ta taya mutumin raino.

Yarinyar ta ce mutumin ya haike mata ne a lokacin da matarsa ta yi balaguro zuwa Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel